Rahaf Mohammed al-Qunun 'yar kasar Saudiyya da ta kaurace wa 'yan uwanta a karshen mako ta roki kasashen Canada, Australia da kuma Birtaniya da su ba ta mafaka.
Rahaf ta ki yadda ta hau jirgi daga birnin Bangkok na kasar Thailand zuwa Kuwait a ranar Litinin, sannan kuma ta kulle kanta a dakin hotel din filin jirgin saman.
Ta bayyana cewa tana tsoron 'yan uwanta za su iya halaka ta saboda barin addinin musulunci da ta yi, inda yanzu dai take karkashin kulawar majalisar dinkin duniya.
Ana yanke wa wanda ya yi ridda hukuncin kisa ne a kasar saboda haka hukumomin Thailand suka shawarce ta da ta koma kasar Kuwait inda 'yan uwanta suke.
Budurwar ta ja hankalin mutane da dama a shafukan sada zumunta, inda ta yi ta turo bayanai kai-tsaye na abinda ke faruwa da ita a shafinta na Twitter kuma ta samu mabiya dubu 50,000 a kasa da kwana biyu.
"Rayuwata na cikin hadari, 'Yan uwana sun yi barazanar kashe ni," Rahaf ta shaida wa Reuters.
Ta wallafa a shafinta na Twitte a ranar Lahadi cewa "Ina neman mafaka a kasashen Canada, da Amurka, da Australia, da kuma Burtaniya. Ina nema wakilansu da su tuntube ni".
Wani jami'in harkokin kasar waje na kasar Australia ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, kasarsa za ta ba wa Rahaf mafaka da zarar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta gama bincike.
Kasar Thailand ba ta cikin kasashen da suka amince da yarjejeniyar majalisar dinkin duniya kan 'yan gudun hijira, sai dai shugaban hukumar shige da fice na kasar ya ce kasarsa ba za ta mika ta ga Saudiyya ba.
0 Comments:
Post a Comment