Friday, 11 January 2019




Buhari ya jinjina wa BBC a kan tsage gaskiya

Home Buhari ya jinjina wa BBC a kan tsage gaskiya

Anonymous

Ku Tura A Social Media
[post by samaila umar lameedo]

Buhari ya jinjina wa BBC a kan tsage gaskiya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa kafar watsa labarai ta BBC saboda tsage gaskiya komai dacin ta.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne lokacin da shugaban Sashen BBC mai watsa shirye-shirye ga duniya, Mr Jamie Angus, da tawagarsa suka kai masa ziyara ranar Laraba a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar.
"BBC ta yi fice wurin bayar da labarai ba tare da karin gishiri ba" musamman irin rawar da ta taka lokacin yakin basasar Najeriya, in ji Shugaba Buhari.
Zaben 2019: Tawagar BBC ta isa jihar Nasarawa
Ma'aikaciyar BBC ta kashe kanta
Ya yaba wa Sashen Hausa na BBC kan yadda yake bayar da labarai a yankunan Sahara, da kuma kokarin da BBC ta yi na bude sabbin sassan a yarukan Yarbanci.
Ya yi kira ga kafofin watsa labaran kasar su guji bayar da labaran karya wadanda ka iya jefa kasar cikin rikici.
A nasa jawabin, Mr Angus, ya shaida wa shugaban kasar cewa tawagarsa ta kai wa shugaban ziyara ce domin ta shaida masa irin shirye-shiryen da take yi na kawo labarai da rahotanni game da zaben Najeriya da za a yi a watan gobe.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: