Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Sani Usman ya ce sojojin kasar tare da sauran jami'an tsaro sun mamaye ofisoshin kamfanin jaridar don "gayyatar wasu ma'aikatan gidan game da wani labari da aka buga a jaridar ranar Lahadi."
Sani Usman ya ce "labarin ya kunshi wasu muhimman bayanan sirri na rundunar wanda zai iya yin zagon kasa ga tsaron kasa."
Mai magana da yawun rundunar dai ya zargi jaridar da bayyana abin da rundunar ke shiryawa dangane da ayyukanta a kan Boko Haram.
Ya kuma ce labarin ya bankado wasu muhimman abubuwa da rundunar ke shirya wa da zai amfani 'yan Boko Haram.
Da yammacin Lahadi ne, mai magana da yawun Shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya ce gwamnatin kasar ta umarci rundunar da ta fita daga ofishin jaridar, kuma su tattauna a tsakaninsu don samun maslaha.
Sojoji dauke da makamai ne suka afkawa babban ofishin Daily Trust da ke unguwar Utako a Abuja ranar Lahadi, inda suka kwashe kayan aiki kuma suka rufe duka ma'aikatan a wani daki a cikin ofishin.
Hakan dai ya faru ne bayan da sojoji suka je ofishin kamfanin da ke Maiduguri, jihar Borno inda suka kama Editan yankin, Uthman Abubakar da wani wakilin jaridar Ibrahim Sawab.
An fara buga jaridar Daily Trust dai mai zaman kanta ne a shekarar 1998 a Najeriya.
Wani ma'aikacin Daily Trust ya shaida wa BBC cewa: "Bayan da jami'an tsaron suka kori duka ma'aikatan daga ofishin, ciki har da mai tsaron wurin, sai suka rufe ofishin na Borno. "
"Sai muka yi kokarin jawo hankalin shugaban sojojin don jin dalilin da ya sa suka shigo ofishin amma ya ki ya yi magana."
"Daga baya suka yi dirar mikiya a ofishimu na Abuja."
"Zatonmu dai shi ne wannan farmakin yana da alaka da labarin da muka buga ranar Lahadi."
"Mun yi wani labari da ya fitar da bayanan ayyukan soji a arewa maso gabashin Najeriya."
Wannan dai ba shi ne karo na farko da rundunar soji ta kai sameme kamfanin ba.
A shekarar 2015, daf da zaben shekarar rundunar ta yi dirar mikiya a ofishin jaridar da wadansu kamfanonin jarudun kasar.
0 Comments:
Post a Comment