Wednesday, 2 January 2019




Mamman Nasir: Marigayi Shehu Shagari ba shi da riko

Home › › Mamman Nasir: Marigayi Shehu Shagari ba shi da riko

Anonymous

Ku Tura A Social Media

Ministan Shari'ah a tsohuwar majalisar arewa, Justice Mamman Nasir, Galadiman Katsina, ya bayyana marigayi Alhaji Shehu Aliyu Shagari da mutum ne mai jan girmansa da rashin riko.

Mamman Nasir yace kasancewar sun yi karatu tare a tsohuwar Kwalejin Katsina, Barewa a yanzu marigayi Shehu Shagari na cikin shugabannin dalibai.

Ya kuma ce dukkan malaman makarantar na matukar girmama shi, saboda ba shi da wata dagawa, ko kuma irin kinjin nan na samari.
"Yayi mun mai unguwa Lekot a kwaleji, saboda yana cikin dalibai masu da'a dan ban taba gani ko jin cewa ance yayi rashin jin nan na 'yan makaranta ba. Sannan yana gama makaranta ya taba koyarwa, sannan kuma ban taba jin wani yace yayi wata tsiwa ko ace ga abokin fadansa ne ba".

Ya kara da cewa, "Yana daga cikin minitocin da Tafawa Balewa ya amince dasu, idan akwai wani abu da ake san ayi cikin sirri, shi firai minsta ke aikowa wajen Sarduna, kuma in ma wani abu za'ai shi za'a saka, saboda haka mutum ne shi mai rikon amana"
Mutuwar tsohon shugaban Nijeriya a jamhuriya ta biyu, Alhaji Shehu Aliyu Shagari, ta tafi da daya daga cikin fitattun 'yan mazan jiya kalilan da suka rage, wadanda suka ga Jamhuriya ta daya a Najeriya.

Ya ce ko a lokacin da marigayi Shehu Shagari ya tsaya takarar shugabancin kasar, dattakunsa ne yasa irinsu Galadiman Katsinan suka jajirce wajen ganin an janye masa, saboda shi ne babba a tsakanin Danmasani da Adamu Fika,

Justice Mamman Nasir, Galadiman Katsina, ministan shari'ah a tsohuwar majalisar arewa, ya bayyana marigayi alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari a matsayin dattijo mai dattako wanda bashi da ruko:

"Yana daga cikin mutanen da ake girmama su, domin dukkan abin da kaga Shagari a ciki abu ne sahihi, shi yasa ake girmama shi, domin mu biyu muka rage da muka yi ministoci zamanin Sarduna da firai minista Abubakar Tafawa Balewa, a domin haka samarin Sarduna da ake kiranmu, yanzu mun zama manya, Alhamdulillahi."
@bbchausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: