Messi ya zama dan kwallo na farko da ya ci kwallaye 400 a La Liga
Lionel Messi ya ci kwallo 400 a gasar La Liga, bayan da Barcelona ta doke Eibar da ci 3-0 a gasar mako na 19 da suka kara a ranar Lahadi.
Luis Suarez ne ya ci sauran biyun da ya bai wa Barcelona damar samun maki biyar tsakaninta da ta biyu a teburin La Ligar bana.
Da wannan kwallon da Messi ya ci ya tsawaita tarihin cin kwallaye a gasar ta La Liga - Cristiano Ronaldo ne keda kwallaye fiye da 300 a fafatawa 435 da ya yi wa Real Madrid.
Messi wanda ya buga wa Barcelona wasa 22 a kakar 2018/19 ya ci kwallo 23, ciki har da 17 da ya zura a raga a gasar La Liga, kuma shi ne kan gaba a Spaniya.
Barcelona za ta karbi bakuncin Levante a wasa na biyu a Copa del Rey a ranar 17 ga watan Janairu, a wasan farko Levante ce ta yi nasara da ci 2-1.
BBChausa.
Monday, 14 January 2019
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Ta yaya mutum zai halarci shirin horar da kwallon kafa a TuraiTa yaya mutum zai halarci shirin horar da kwallon
Solksjaer ba shi da farin ciki da Fellaini, zai iya buga wasan tsakiya a JanairuSolksjaer ba shi da farin ciki da Fellaini, zai i
Liverpool ta bada tazarar maki 7 a saman teburin Frimiya da kyarLiverpool ta bada tazarar maki 7 a saman teburin
City ta ci gaba da kankane teburin PremierManchester City ta je ta doke Watford 2-1 a wasan
Real Madrid a hankali a hankali tana cire Cristiano Ronaldo daga tarihin su.Real Madrid a hankali a hankali tana cire Cristia
Zargin Fyade: Juventus ta tafka babbar asara sadaniyyar Ronaldo: E. A Sports ta goge hotonshi daga shafintaTauraron dan kwallon kafa na Juventus na kara shi
0 Comments:
Post a Comment