Monday 21 January 2019




Pictures:- Hotunan Maryam Gidado Da Yaja Mata Zagi Wanda Ibrahim Mai Shinku Ya Dafa Kafadarta

Home Pictures:- Hotunan Maryam Gidado Da Yaja Mata Zagi Wanda Ibrahim Mai Shinku Ya Dafa Kafadarta

Anonymous

Ku Tura A Social Media
             
Dafawar da Ibrahim Mai Shunku yayiwa jaruma Maryam Gidado yaja mata zagi a shafinta na instagram.
A shekaran jiya ne dai jaruma Maryam Gidado ta daura hoton da Jarumi Ibrahim Mai Shunku ya dafata a shafinta na instagram inda da yawan mutane suka tofa Albarkacin bakunan su.
              
Wayansu sun bata shawara akan ta cire hoton wasu kuma zagi ne ya biyo baya wasu kuma babu abun ya fito daga bakinsu sai aibata yan masana’antar fina-finan Hausa cewa dukan su yan iska ne.
Hakan ne ya tilasta jarumar cire hoton a shafinta, idan bamu manta ba kwanakin baya irin wannan ya faru da jaruma Rahama Sadau da General Ballo Muhammad Bello ya dafata hakan kuma yajawo mata zagi a kafafen sada zumunta.
Bahaushe na cewa gani ga wane ya isa wane tsoron Allah to shin jaruma Maryam Gidado bata da labarin abun da ya faru da yar uwan nata ne?
Yan uwa mabiya wannan shafi namu mai Albarka ya kuka ganin wannan halayya da yan film din sukeyi na namiji ya dafa mace hakan ya dace kuwa?
Ku Kasance Tare Da Shafin Duniyarfim.com Domin Samun Labarai Da Dumi-duminsu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: