Buhari mayen mulki ne - Atiku
Dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari dan kama-karya ne.
Alhaji Atiku ya bayyana haka ne a wurin taron da jam'iyyar PDP ta gudanar a Abuja ranar Talata.
Sai dai Shugaba Buhari da jam'iyyarsa ta APC ba su ce komai ba kan wannan zargi ba tukuna.
"Na sha fada cewa idan ana magana a kan mulkin dimokradiyya, Janar Buhari bai yarda da shi ba, bai taba yarda da dimokradiyya ba. Mu ne muka fara fafutukar korar soja domin dawo da dimokradiyya. Bai taba shiga fafutikar dawo da dimokradiyya ba.
"Kuma kamar yadda kuke ganin, ya ari rigar dimokradiyya ya sanya ne kawai domin ya samu mulki ya yi abin da yake yi yanzu; Ya fi kama da dan kama-karya, ba dan dimokradiyya ba," in ji dan takarar shugabancin Najeriyar.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi zargin cewa jam'iyyar APC ta tura wasu mutane kasar China inda suka samu horo kan yadda za su hana na'urar Card Reader "yin sauri" a yankuna da PDP ke da magoya baya da yawa, sannan a sa "na'urar ta yi sauri "a bangarorin da APC ke da magoya baya da yawa.
A cewarsa, "Idan mutum daga yankin kudu masu kudu ko kudu maso gabas ko kuma arewa ta tsakiyar kasar yake, mai yiwuwa ku fuskanci Card Reader maras sauri;
"Amma masu kada kuri'a a yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabas da kuma kudu maso yamma, mai yiwuwa Card Reader din su ta yi saurin tantance su. Mun tattara wadanna bayanai mun mika ga kwamitin yakin neman zabe domin su dauki mataki."
Atiku kuma ya zargin Shugaba Buhari da son mulki ido rufe. Ya ce "Na sha fada cewa Janar Buhari ba mai bin dimokradiyya ba ne. Bai yarda da dimokradiyya ba, zancen baka ne kawai. Buhari mutum ne mai son mulki" a cewarsa.
Atiku Abubakar ya yi kira ga jami'an tsaron kasar da kada su yi biyayya ga kiran da Shugaba Buhari ya yi cewa duk wanda ya saci akwatin zabe, to a bakin ransa.
Ya ce hakan ya saba da kundin tsarin mulkin kasar.
0 Comments:
Post a Comment