Friday 22 February 2019




INEC Ta Bi Umurnin Kotu Ta Anshi Yan Takarar Jam'iyyar APC Na Jihar Zamfara

Home INEC Ta Bi Umurnin Kotu Ta Anshi Yan Takarar Jam'iyyar APC Na Jihar Zamfara

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa za ta yi aiki da umurnin kotun daukaka kara dake zamanta a birnin tarayya Abuja da ta soke hukuncin babbar kotun tarayya da ta hana a saka yan takarar jam'iyyar APC a jihar Zamfara bisa gaza aiwatar da zaben fitar da gwani da hukumar zabe INEC ta bayar da adadin kwanakin kaidar da ya kamata a kammala shi.
A sanarwar da INEC din ya yi a shafinta na Twitter ta ce a yanzun yan takarar jam'iyyar APC tun daga matakin Gwamna da yan majalissar tarayya da kuma na jihohi za a kara da su a cikin zaben da za a fara gudanarwa daga gobe Asabar 23 ga watan February 2019
Sai dai hukumar zaben ba ta bayyana bangaren ko wadanne yan takarar ne za ta saka a cikin zaben ba, kasantuwar yadda yan bangaren Gwamnan jihar mai barin gado Abdulaziz Yari, da bangaren Sanata Kabiru Marafa kowa ke bayyana cewa yan takararsa ne ke kan kaida.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: