Tuesday 26 February 2019




Muhimman abubuwa 5 da suka faru a zaben Najeriya.

Home › › Muhimman abubuwa 5 da suka faru a zaben Najeriya.

Anonymous

Ku Tura A Social Media





A ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu ne 'yan Najeriya suka kada kuri'unsu na zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin tarayya.


Sashen Hausa na BBC ya kawo muku rahotanni da bayanai da sharhi kai-tsaye kan yadda zaben ya gudana daga sassan Najeriya.
Mutane sama da 70 suka fafata a zaben shugabancin kasar inda kimanin mutane 6,300 suka nemi lashe kujerun majalisar dokokin tarayya.
Hukumar zaben Kasar ta ce kimanin mutum miliyan 84 suka isa yin zabe inda sama da mutum miliyan 72 suka yi rajista.


Harbe-harbe a jihohin Borno da Yobe







An samu harbe-harbe a waje-wajen Maiduguri, babban birnin jihar Borno da kuma a Geidam a jihar Yobe.
Wakilinmu a jihar ya tabbatar mana da jin harbe-harbe a wasu sassan na Maiduguri.
A Jihar Yobe bayan fara harbe-harbe a Giedam, mutane sun fara fita suna tserewa daga gidajensu suna barin cikin garin.
Hakan ne ya sanya gwamnan jihar, Ibrahim Geidam ya fasa fita kada kuri'arsa saboda shawara a kan tsaro da jami'an tsaro suka ba shi kamar yadda mai taimaka ma sa ya bayyana
Amma duk da haka mutane sun fito kuma sun kada kuri'unsu.




Fara zabe a kan lokaci

 


 


Masu kada kuri'u a jihohin Ekiti da Adamawa da Taraba da wasu jihohin sun yi sammako domin zuwa kada kuri'unsu da safiyar asuba tun kafin gari ya fara wayewa.
A jihar Adamawa a rumfar zabe ta Shagari Clinic da ke a Bole/Yolde Pate a Yola, sun fito tun kafin wayewar gari kamar yadda aka tabbatar mana.
Masu kada kuri'a a Shagari Quarters da Kundila a jihar Kano kuwa sun fito da wuri inda har sai da suka jira sannan aka kawo kayan zabe.
Haka zalika masu zabe a rumfar Gajawa ta 1 da 2 sun yi sammako domin gudanar da zabe.
A Owerri kuwa, jama'a sun fito kasuwancinsu inda wasu suka ringa fita da abin hawa.


Atiku da Buhari a mazabunsu

 


Atiku ya kada kuri'arsa a mazabar Ajiya mai lamba 02 da ke a Arewacin Yola da misalin karfe 11 zuwa 12 na safe.
A bangare guda kuwa, Shugaba Buhari ya isa mazabarsa da misalin karfe 8 zuwa 9 na safe.
Shugaba Buhari ya isa tare da matarsa Aisha Buhari inda suka yi zabe.
Bayan da ta dangwala kuri'arta, Buhari ya yi wani abin da ya ja hankulan mutane musamman masu amfani da shafukan sada zumunta inda aka ga ya kalli ko mai dakinsa wa ta zaba.

Atiku ya tafi tare da matarsa Titi inda suka jefa kuri'unsu a tare.



Wa ya lashe mazabarsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi nasarar lashe zabe a mazabar babban abokin hamayyarsa, Aiku Abubakar inda ya samu kuri'u 186 shi kuma Atiku ya samu 167.

Shi kuma Atiku Abubakar ya yi nasarar lashe kuri'un daya daga cikin rumfunar zabe biyu na fadar shugaban kasa da ke a Abuja.
Atiku ya samu kuri'u 525 shi kuma Buhari ya samu 465 a rumfa mai lamba 022 a fadar shugaban kasa dake a babban birnin tarayyar kasar, Abuja.
Buhari ya yi nasarar lashe kuri'u a rumfunan zaben Obasanjo da Dankwambo da gidan gwamnatin jihar Sakkwato.
Buhari kuma ya yi nasara a mazabar daya daga cikin abokan hamayyarsa dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar SDP, Donald Duke.


Shi kuma mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya fadi a mazabarsa ta Ward 4 dake a jihar Legas inda PDP ta samu kuri'u 387, ita kuma APC ta samu 197.





Peter Obi, dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP ya yi nasarar lashe kuri'un rumfar zabensa.





Kazalika, tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kai bantensa a akwatun zabensa. Jam'iyyarsa ta PDP ta lashe zaben shugaban kasa da kuri'a 156, yayin da jam'iyyar APC ta samu kuri'a 72.







Tsoffin Shugabanni

 

Yadda tsoffin shugabannin kasa suka fito suka kada kuri'arsu musamman Goodluck Jonathan da Olusegun Obasanjo da Abdulsalami Abubakar an ta yin kokarin gano dan takarar da suka zaba musamman Obasanjo da ya dawo yana goyon bayan tsohon mataimakinsa Atiku Abubaka tare da caccakar gwamnatin APC ta Buhari.

Rikicin zabe

An samu haren-harbe a wasu rumfunan zabe a wasu jihohin kudu maso yammacin Najeriya.
Wasu rahotanni sun ce rikicin ya hana gudanar da zabe a wasu mazabu na jihar Lagos da Anambra da kuma jihar Rivers.
An kona takardun zabe saboda hatsaniyar da aka samu.
Kammala zabe cikin lokaci

An yi nasara gama zabe da wuri ido na ganin ido.
Sabanin zaben 2015 wanda aka fara da tantance mutane sannan daga baya aka yi zabe, zaben 2019 ana tantancewa ana yin sa.
Gama zabe da wuri ya sanya muka samu kawo muku sakamako a mazabar Atiku da ta Buhari.
Wannan zabe ya zo ne bayan da aka dage shi daga ranar da aka shirya yin sa a farko, watau 16 ga watan Fabrairu da hukumar zabe ta kasa INEC ta fara niyyar yin sa.
Samun sauya takardun kada kuri'o'i na wasu jihohin akai wasu da wasu dalilai ne ya yi sanadiyyar dage zaben zuwa 23 ga watan Fabrairun domin a samu a gudanar da sahihin zabe.
Wannan shi ne karo na uku cikin shida a jere da aka dage zaben kasar tun bayan dawowar damakaradiyya a 1999. Da Ga www.HausaSite.cf

 















 







Share this


Author: verified_user

0 Comments: