Friday 22 February 2019




'Yan sanda ke tsaron rumfar zabe ba sojoji ba - INEC

Home 'Yan sanda ke tsaron rumfar zabe ba sojoji ba - INEC

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce 'yan sanda ne ke da hakkin kula da rumfunan zabe ba sojoji ba.
Shugaban hukumar INEC ne Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a lokacin yake bayani kan shirin zabe da kuma amsa tambayoyi a ranar Alhamis.
An tambayi shugaban INEC ne kan irin rawar da sojoji za su taka a ranar zabe, sai ya amsa da cewa tsarin da aka sani shi ne, ba hakkin sojoji ba ne kula da tsaro a rumfunan zabe, amma ya danganta da gayyatar da suka samu daga 'yan sanda.
Ya ce hukumar INEC na aiki ne da hukumar 'yan sanda amma idan suna fuskantar wata barazana suna iya gayyato sauran jami'an tsaro da suka hada da sojoji domin su taimaka.
"Sojoji na iya yin aikin da ya rataya a wuyan 'yan sanda a wurin zabe idan har 'yan sandan sun gayyace su."
"Ya danganta da barazanar da ta taso amma aikin tabbatar da tsaro a rumfunan zabe aikin 'yan sanda ne," in ji shugaban hukumar INEC.
Wannan na zuwa ne bayan babban hafsan sojin kasa na Najeriya Janar Tukur Buratai, a ranar Laraba ya bayyana rawar da sojoji za su taka a ranar zabe.
Yayin da yake gana wa da manyan jami'ai da kwamandojin sojin kasar, Janar Burutai ya yi umurni ga kwamandojinsa su dauki mataki na ba sani ba sabo kan duk wanda ya nemi dagula sha'anin zabe a kasar.
Ya ce rundunar sojin kasar ta dauki mataki kan satar akwati da kayayyakin zabe da aka saba yi a zabukan baya.
Tun da farko shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi gargadi ga barayin akwatin zabe inda ya umurci jami'an tsaron kasar daukar matakin ba sani ba sabo na rashin tausayi ga duk barawon akwatin zaben da suka kama.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: