Friday 5 April 2019




An karrama Musulman da aka kashe a masallaci a New Zealand

Home › › An karrama Musulman da aka kashe a masallaci a New Zealand

Anonymous

Ku Tura A Social Media
An gudanar da wani taron zaman makoki a birnin Christchurch wanda kuma aka watsa a akwatunan talabijin a duk fadin New Zealan domin karrama mutum 50 da wani dan bindiga ya kashe lokacin da suke sallar Juma'a ranar 15 ga watan Maris.
Farai Minista Jacinda Ardern ta yi jawabi a wajen taron, haka su ma wasu jagorin musulmai da wadanda suka tsallake rijiya da baya.
Mawakin nan da ya Musulunta Yusuf Islam dan Birtaniya, wanda a da sunansa Cat Stevens ya rera wakar nan tasa ta zaman lafiya, Peace Train, a taron.
Sama da mutum 20,000 ne suka halarci taron a dandalin Hagley Park, bisa tsauraran matakan tsaro.




Da take magana a masallacin Al Noor, inda aka kashe sama da mutum 40, Ms Ardern ta ce New Zealand tana da alhakin tabbatar da cewa ta kasance wajen da kowa zai yi rayuwar da ya zaba.
Ta ce, New Zealand ba ta da kariya daga kwayar cutar tsana, amma kila za ta zamo wadda ta samu maganinta a yanzu.
Gaba daya mutum 50 ne suka mutu ranar 15 ga watan Maris yayin da wani mai tsanin akidar fifita farar-fata ya kai hari kan wasu masallata mako biyu da suka gabata.
Wakilan gwamnatoci da dama ne daga fadin duniya suka halarci taron karrama mamatan, cikin wandanda suka halarta kuwa har da faraministan Australia Scott Morrison.


Farid Ahmed, daya dgaa wadanda suka tsira a harin na Christchurch. 



Farid Ahmed, wanda ya tsallake rijiya da baya a harin da dan bindigar ya kai, to sai dai an kashe matarsa Husna, amma duk da haka ya ce yana neman zaman lafiya, kuma ya yafe wa dan bindigar.
"Ya ce, ba na son zuciyar da ta ke tafarfasa tamkar dutse mai aman wuta. Ina son zuciya ne mai cike da kauna da bayar da kulawa kuma tausayi."

Share this


Author: verified_user

0 Comments: