Friday 5 April 2019




Onnoghen wanda aka dakatar ya mika takardar murabus

Home › › Onnoghen wanda aka dakatar ya mika takardar murabus

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Alkalin Alkalan Najeriya Walter Onneghen, wanda aka dakatar, ya mika takardar murabus zuwa ga fadar Shugaban kasar Najeriya.
Wata majiya a fadar shugaban kasa da ba ta yadda a ambaci sunanta ba ta tabbatar wa da BBC cewa ya mika wasikar.
Sai dai kuma babu sanarwa a hukumance daga fadar, a yayin da Shugaba Muhammadu Buhari yake halartar taro a yankin gabas ta tsakiya.
A bisa tsari dai, da zarar wanda yake da alhakin cirewa da nadawa ya karbi wasikar murabus daga hannun mai neman yin murabus din take hukuncin zai fara aiki.
A ciki wannan makon ne hukumar kula da harkokin shari'a ta kasa NJC ta bai wa Shugaba Buhari shawarar yi wa Onnoghen ritaya.
Walter Onnoghen dai yana fuskantar shari'a ne a gaban kotun da'ar ma'aikata, inda ake zarginsa da yin karya kan kadarorin da ya mallaka yayin kama aikin Alkalin Alkalan Najeriya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: