Wednesday 3 April 2019




Valencia ta doke Real Madrid

Home › › Valencia ta doke Real Madrid

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Valencia ta yi nasarar cin Real Madrid 2-1 a wasan mako na 30 a gasar cin kofin La Liga da suka fafata ranar Laraba.
Goncalo Guedes ya ci wa Valencia kwallon farko saura minti 10 a je hutun rabin lokaci, sannan Ezequiel Garay ya kara na biyu saura minti bakwai a tashi daga karawar.
Wannan ne karon farko da Zinedine Zidane ya yi rashin nasara tun bayan da ya karbi aikin horas da Real karo na biyu, ya ci Celta Vigo da Huesca.
Da wannan sakamakon Valencia ta koma mataki na biyar kan teburin La Liga da maki 46, Real tana nan a matsayinta na uku da maki 57.
Barcelona ce ta daya da maki 70, sai Atletico Madrid mai maki 62 ta biyu a kan teburin La Liga.
Sauran sakamakon wasannin mako na 30 da aka yi:
  • Athletic Bilbao 3 - 2 Levante
  • Eibar 2 - 1 Rayo Vallecano
  • Huesca 3 - 3 Celta de Vigo
Sauran wasannin Real Madrid da suka rage
15 Afirilu 2019
  • Leganes da Real Madrid
21 Afirilu 2019
  • Real Madrid da Ath Bilbao
25 Afirilu 2019
  • Getafe da Real Madrid
28 Afirilu 2019
  • Rayo Vallecano da Real Madrid
05 Mayu 2019
  • Real Madrid da Villarreal
12 Mayu 2019
  • Sociedad da Real Madrid
19 Mayu 2019
  • Real Madrid da Real Betis


Share this


Author: verified_user

0 Comments: