Wednesday 3 April 2019




Wata mata ta haihu a kan bishiyar mangwaro saboda ambaliya

Home Wata mata ta haihu a kan bishiyar mangwaro saboda ambaliya
Ku Tura A Social Media




Wata mata ta haihiwa akan bishiyar mangwaro yayin da take neman tsira daga ambaliyar ruwan da ta jawo mahaukaciyar guguwar Idai a tsakiyar Mozambique.
Amélia wadda ba ta da miji ta haifi 'yarta Sara yayin da take saman bishiyar tare da danta mai shekara biyu.
Bayan kwana biyu ne makwabta suka ceto su, bayan da aka yi wata matsananciyar guguwa da ta jawo mutuwar mutum 700.
Hakan na zuwa ne bayan kusan shekara 20 da haihuwar wata jaririyar Rosita Mabuiango da ita ma aka haife ta a kan bishiya a kudancin Mozambique.
"Ina gida tare da dana mai shekara biyu a yayin da kwatsam ba tare da gargadi ba ruwa ya fara ambaliya cikin gidan," kamar yadda ta shaida wa Asusun Kul da Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF.
"Ba ni da zabi sai na hayewa bishiya, daga ni sai dana."
Amélia da sabbin iyalanta da suka ba ta mafaka a yanzu suna zaune ne a Dombe na wucin gadi, kuma rahotanni sun ce suna cikin koshin lafiya.
Labarin Rosita Mabuiango, mai shekara 19 a yanzu, ya mamaye kanun labarai a duniya bayan da ita da da mahaifiyarta Sofia bayan da aka ceto su a helikwafta daga kan bishiyar da ruwa ya mamaye.
Da take magana da wata jaridar kasar, Sofia ta ce"haihuwar na da matukar ciwo."
"Na yi ta kuka da ihu. Wani lokacin na kan yi zaton haihuwar ce ta taho, amma wani lokacin sai na zaci yunwa ce."
Ta kara da cewa: "Mutane da dama sun rasa komai nasu sakamakon ambaliyar, amma ni na samu wani abu (jaririryar da na haifa).









 Rosita Mabuiango ma a kan bishiya aka haife ta a shekarar 2000 a Kudancin Mozambique sakamakon ambaliya da ta rutsa da mahaifiyarta




Amma a hirarta da BBC, Rosita ta ce alkawuran da gwamnati ta yi min na daukar nauyin karatuna da yin bulaguro zuwa Amurka da gwamnatin Amurka ta yi duk ba a cika su ba.
"Mahaifiyata ce ke daukar nauyin karatuna, ba abun da na samu daga gwamnati," in ji Rosita.
"To, gwamnati ta gina mana gida amma gidan duk ya lalace. Idan ana ruwa, yana yoyo. A kalla ai da za su taimaka su gyara mana."

Share this


Author: verified_user

0 Comments: