Showing posts with label Dadin kowa. Show all posts
Showing posts with label Dadin kowa. Show all posts

Thursday, 7 February 2019

MALAMAN ALKUR'ANI SUN YI JAN KUNNE GA TASHAR AREWA24 Cikin Shirin (DADIN KOWA)

MALAMAN ALKUR'ANI SUN YI JAN KUNNE GA TASHAR AREWA24 Cikin Shirin (DADIN KOWA)

Muna kallon shirin dadin kowa Muna kallon yadda kuka shirin Yaki da Malaman AL-QURANI domin tozarta ALMAJIRCI Ta hanyar dora malam NA TA'ALA (MATO YAKUBU) da bashi damar tozarta AL QUR'ANI kai tsaye domin wata manufa ta yahudu akan Almajirci da nunawa wadanda ba musulmai ba su fahimci dukkan malamin AL QUR'ANI a matsayin mutum me son zuciya da son kai wadda bai isa akan komai ba.
JAN KUNNE
A matsayin mu makusanta makaranta AL- QUR'ANI muna kira da babbar murya cewa ya zama dole a gyara ko kuma muma mu daura dammarar yaki daku a makarantun mu na zaure da tsangayu da islamiyyu ta hanyar aika muku da ADDUO'I na musamman har sai ALLAH YAYI MANA MAGANINKU.
JAN KUNNE GARE KA WATO YAKUBU (NA TA'ALA) (Allah Ya Shirya).
Ya zama dole ka gyara irin siffofin da kake siffanta makaranta AL QUR'ANI domin cimma manufarka ta tozarta malaman AL QUR'ANI da wulakantasu ka sani cewa ka shirya fito na fito ne da LITTAFIN ALLAH dukkan wadda ya shirya haka babu shakka ya durfafi hanyar fito na fito ne da MAHALICCIN WANNAN LITTAFI ALLAH (SWT).
KIRA GA MUTANE MUSAMMAN MA MAKARANTA AL- QUR'ANI Mutaimaka Wajen Yada Wannan Saqo Har Ya Isa Ga Masu Shirya Wannan Shiri Wato Hukumar Gidan Area24.
Muhammad Ahidan Bako Arifullah
Allah Ya Kwauta.

Saturday, 5 January 2019

Video- Dadin kowa sabon salo epsode 87

Video- Dadin kowa sabon salo epsode 87



Domin kallon cigaban shirin dadin kowa sabon salo na satin da ya wuce.

ACIKIN WANNAN SATIN

A yayin da Kamaye ya fado daga saman bene ya wuce cikin injin markada siminti, bayan an wuce dashi asibiti rai kokai mutu kokai, a cikin wannan yanayin Adama na zaune a gida tana ci gaba da kulle kullen aurar da Hannatu ga Ayuba Maigadi domin gujewa abin kunya, shin wanan auren zai yuwu ?

Saturday, 8 December 2018

Video- Dadin kowa sabon salo epsode 83

Video- Dadin kowa sabon salo epsode 83




lokacin da Hansatu ke murnar dawowarta gidan mijinta da ta jima tana biko wato Mal. Musa, wani babban lamari ya faru da ita wanda ya sakata dana sanin dawowarta gidan. Yayin da a gefe guda Kawu Mala ya yi amai ya lashe abinsa, don ganin yanda za ta kaya mu hadu a kashi na 83 na Dadin kowa sabon salo.

Saturday, 6 October 2018