Showing posts with label Girke Girke. Show all posts
Showing posts with label Girke Girke. Show all posts

Saturday, 22 December 2018

Banana Gel

Banana Gel

BANANA GEL
1 Banana
2 milk
3 flavour
4 sugar
Method:
Kisamu cokali kiyi mashing tare da ruwa kadan ayabannaki
zaki Iya blending a blender sannan kisamu rariya ki dunga
zubawa da cokali yana sauka a roba daban har kigama sekin
tabbatar Babu gudajen ayaba aciki seki dauko garin
madaranki kizuba ki juya kisa banana flavour da sugar ki
hada shi sosai Ba ruwa ruwa Ba kisa a fride zezama semi
liquid haka.
Note: in zakiyi anfani da madaran ruwa acikin banana kada
kisa ruwa.
07069332689
DAMBUN SHINKAFA:Girke Girke

DAMBUN SHINKAFA:Girke Girke

DAMBUN SHINKAFA
Kayan hadi
Shinkafa
Zogale
Mai
Tattasai
Albasa
Nama ko kifi
Maggi
Gishiri
YADDA ZAKI HADA
GIDAN ABINCI DA NOVELS
07069332689
Ki bada a barzo shinkafa saiki sa rariya tankaden gari ki fidda
gari Dan kar dambun ya hade. Saiki wanke shinkafar da aka
barza ki yanka nama kanana cikin ta saiki zuja su hade ki
zuba ga abunyin dambu, Saiki yanka tarugu albasa da tattasai
ki hada da zogale ki wanke. Saiki kwashe danbun da kika
Dora a wuri mai fadi ki zuba su zogale da maggi da gishiri
kiyayyafa ruwa ki juya suhade ki mayar ya qara turara idan
yayi ki sauke kiss mai shikenan. Amma idan da steamer
zakiyi komai zaki zuba a shinkafar ki zuba. Amma idan da
abun yi na gargajiya zakiyi yafi kyau ayi bugu 2 yadda nayi
bayani. Kuma idan kinaso zaki iya sa su karas,nidai da kifi
nayi amfani aci lyf.
GIDAN ABINCI DA NOVEL
07069332689
Yanda Ake Gullisuwa

Yanda Ake Gullisuwa

GULLISUWA
Madara
Sugar
Baking powder
Kisamu abu mekyau ki juye madaranki kizuba sugar akai
kibarbada banking powder kadan sai ki kwaba da ruwan
dumi da dantauri sai ki mulmulata idan ta sha iska sai ki
soya
GIDAN ABINCI DA NOVELS
WhatsApp: 07069332689
Burodin Ayaba:Girke Girke

Burodin Ayaba:Girke Girke

arkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin
koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin
ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma
don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda
muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku
nau’ukan girke-girke daban-daban.
Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a
zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga
da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar
cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu
da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa
hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu.
Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a
saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar,
sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha
ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana
sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.