Showing posts with label Tarihi Daban-Daban. Show all posts
Showing posts with label Tarihi Daban-Daban. Show all posts

Friday, 28 December 2018

Karanta Kaji: Abubuwan da Yakamata Ku Sani game da Marigayi Shehu Shagari

Karanta Kaji: Abubuwan da Yakamata Ku Sani game da Marigayi Shehu Shagari

Bayanan da muka samu daga iyalan tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari ya rasu ranar Juma'ar nan. Tshohon shugaban ya rasu ne a asibitin kasa da ke Abuja inda yake jinya.

Alhaji Shehu Shagari ya rasu yana da shekara 93 a duniya, bayan ya sha fama da jinya.
Ya shugabanci Najeriya daga 1979 zuwa 1983, lokacin da sojoji suka yi gwamnatinsa ta jamhuriya ta biyu juyin mulki, inda Janar Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa.
Alhaji Shehu Shagari yana cikin 'yan siyasar jamhuriya ta farko, da suka yi ministoci a gwamnatin Tafawa Balewa tsakanin 1960 zuwa 1966 da sojoji suka yi wa gwamnatin juyin mulki.
Ya rasu ya bar 'ya'ya 19, maza takwas mata 11 da jikoki da dama.
Gabanin rasuwarsa ya rike sarautar Turakin Sakkwato, wanda babban wakili ne a majalisar koli ta fadar Sarkin Musulmi.
Ya rike wannan sarauta tun daga 1962 har zuwa rasuwarsa.
An garzaya da shi zuwa asibiti a Abuja ne bayan da jikinsa ya yi tsanani a ranar Talata.
Alhaji Shehu Shagari ya sha fama da ciwon Limoniya.
Ana sa ran za a mayar da shi Sakkwato ranar Asabar domin yi masa jana'iza.

KARANTA KAJI: TAKAITACCEN TARIHIN ALH SHEHU SHAGARI

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Wednesday, 26 December 2018

Karanta Kaji: Takaitaccen Tarihin Birnin Lalle da Sarkin Mutum-Mutumi Mai Suna Sarki Kututturu

Karanta Kaji: Takaitaccen Tarihin Birnin Lalle da Sarkin Mutum-Mutumi Mai Suna Sarki Kututturu

Daga abinda marubuci Ɗan Zubairu ya ruwaito, masarautar Birnin Lalle dake can a yankin Dakoro na Jahar Maraɗin Jamhuriyar Nijar, shahararra ce wadda ambaton ta ba zai yanke ba.

Marubuci: Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

Kasancewar Birnin Lalle ɗaya ne daga tsoffin cibiyoyi ga Masarautar Gobir, ana ganin Gobirawa ne suka kafa garin. Amma kuma akwai alamu dake nuna cewar tun da jimawa Birnin Lalle ya kafu, kawai dai gobirawa sun shigo cikinsa ne tare da ƙwace ikon sa.

Birnin ya samo sunansa ne daga yawaitar bishiyoyin Lalle (wanda mata ke kunshi da kuma wanka dashi a baya) dake cikinsa.

Birnin lalle shine birni na gaba da Gobirawa suka sauka tun bayan barowarsu daga Birnin Marandat da Birnin Toro. Da yake daman ance asalinsu daga Baghadaza suke, suka shiga duniya, har kuma a hankali suka rinƙa sauka a garuruwa suna auratayya da yake-yake.. A haka har suka riski birnin Lalle.

Masu cewa gobirawa ne suka kafa wannan birni na Lalle ɗaruruwan shekaru da suka gabata, sun faɗi cewar Gobirawa sun riski wajen ne yana fili sa'ar da suke neman gulbi ko tabki a wannan yanki domin su rinka gudanar da ayyukkan su na noma, kasancewarsu daman bayan yake-yake, sukan jarraba noma tun tale-tale.

Don haka ake ganin da isowar su bakin tabkin sai suka ga bishiyoyin Lalle burjik a zagaye dashi, shine sai suka baiwa wurin suna da cewa “Wannan wuri Birnin lalle kenan!”. Daga nan kuma suka yanke shawarar zama acikin sa.

Amma dai wasu masanan tarihi sun tafi akan cewa Birnin lalle ya kafu ne tun kimanin shekaru 2000 da suka gabata. Sai dai kuma babu takamaimen sunan kabila ko mutanen da suka kafa birnin.

Haka kuma, ana ganin garin ya tumbatsa matuƙa a wani lokaci can a baya, amma ɓarkewar yunwa a wannan birni ce tayi sanadiyyar da Gobirawan suka tashi daga gareshi izuwa birnin Alkalawa dake tsohuwar masarautar Zamfara (wajajen karni na goma sha shidda).

Sai dai duk da haka, ance garin ya sake haɓaka a wajajen ƙarni na goma sha bakwai ta yadda fatake ke isa gareshi fatauci tun daga kano, lokacin ma garin maraɗi na matsayin karamin ƙauye, ko kuma ace sam-sam bai kafu ba.

Ance Sarauniya Tahoua tayi mulkinta a birnin Lalle, ita kuwa itace sarauniya mace ta farko da aka yi a Gobir, kuma itace uwa ga waɗanda suka kafa Biranen konni dake cikin Jihar Tahoua a Jamhoriyar Nijar da kuma Argungu na jahar Kebbin Nijeriya.

Sarki Kanni da Sarki Hammadin shine sunayen 'ya'yayen Sarauniya Tahwa, kuma sun tsira da rayukan sune bayan da suka gudu daga garin da dare, kamar yadda suka shawarta a tsakanin su.

Dalilin hakan kuwa shine, an tilasta musu hawa kan gadon sarautar birnin Lalle ne alhali kuwa basu so.

Hakan kuwa baya rasa nasaba da halin ƙuncin da masarautar ta shiga, na cewar duk wani sarki da aka naɗa mata sai an samu wasu mutane sun bi dare sun halaka shi.

Kanni aka fara naɗawa sarki, dare nayi ya hau sirdi ya ɓace ba’a san inda ya dosa ba. Kashe gari sai aka naɗa ƙanin sa Hammadin, shima kuwa cikin dare ya bi ɗanuwan shi ya gudu.

Ance Hammadin ya ɗan zauna tare da ɗan uwan shi Kanni a birnin Konni tsawon shekaru, daga bisani ya tashi bai sauka ba sai a Argungu.

Mawakin gargajiya kuma masanin tarihi, Marigayi Alhaji Maidaji Sabon Birni ya faɗa a wani baiti cewar duk sa'ar da mahaifiyar Kanni da Hammadin watau Sarauniya Tahwa ta tuno yadda ta rasa 'ya'ayenta, sai ta dugunzuma cikin ɓacin rai, tace “Gobirawa haka kuka kai ni, bani ga Kanni, bani ga Hammadin?”

Amma daga baya ance ta samu haɗuwa dasu bayan an gano mata inda suke. Shine ma akace an kaiwa Sarki Kanni matar shi mai ciki wadda ya gudu ya barta a Birnin Lalle, wasu masoyan sa kuma sukayi dandazo suka tafi gareshi domin zama tare dashi.

Ance Sarki Kanni da ƙanin sa Sarki Hammadin suna da tsagen Gobirawa guda shidda (6) a kuncin su na tsagin hagu, da kuma guda bakwai (7) a tsagin dama, amma da suka haihu sai suka yanke shawarar yiwa kowane yaro tsagu goma (10) a hagu da goma sha-biyu (12) a dama domin bambamta su daga sauran 'yanuwansu Gobirawa.

Game da Sarkin birnin Lalle Kutturu kuwa wanda akan kira shi da suna 'Sarki Dalla Gungume', ya samu shiga cikin jerin sunayen da suka mulki wannan birni duk da kasancewar sa gungumen itace, watau sahun sarakuna irinsu Sarki Barankame, Sarki Kanni, Sarki Bartakeskes, Sarki Hammadin, Sarki Bartuwa-tuwa da wasunsu kimanin ɗari uku da tamanin (380).

Asalin naɗa shi shine, ance akwai wani lokaci a baya, da husumar hawa mulkin Birnin Lalle tayi tsamari a tsakanin Gobirawa dake da iko da garin, ya zamana duk wanda aka ɗora sarki sai masu adawa dashi sunbi dare sun halaka shi komai tsarin sa, don haka sai dabarar sassaƙa gungumen itace a matsayin mutum-mutumi tare da sanya shi cikin ado gami da ɗora shi akan karagar mulki ya faɗo a zukatan manyan fadawan wannan masarauta.

Bayan anyi bikin naɗin Sarki kututturu bisa karagar mulki, rannan sai waɗanda basu so suka sake yin yunkurin kawar da sarkin, kamar yadda suka saba yi ga duk wanda aka naɗa bisa wannan karaga, suka biyo dare ɗauke da makamai, amman sai suka tarar da Sarkin ɗangal-gal bisa karagar shi.
Da yake basu san shirin da akayi ba, sai kurum tunanin su ya basu cewa lallai wannan sarki hatsabibi ne, domin basu san adadin layu ko ƙahunan da ya tanada ba ta yadda ko gezau bai yiba a lokacin da suke fuskantar sa don su halaka shi, sai kurum suka rantaya da gudu.

Tun daga nan kuma aka samu sauki, har kuma aka cigaba da naɗa mutane bisa mulkin Birnin Lalle.

A ɗan lokacin da Sarki Kututturu yayi bisa mulki, waɗanda suka naɗa shine ke gudanar da harkokin mulki gami da zartar da duk wasu lamurori. Har ma an samu cewa idan mutane sunzo yin gaisuwar fada, sai fadawan su amsa da cewa “Sarki ya gaisheka”, don haka ake ganin watakila wannan ne mafarin irin wannan amshin gaisuwa a tsarin Shugabancin Hausawa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

Wednesday, 19 December 2018

Takaitaccen Tarihin Jamhoriyar Kasar Niger: Abubuwan da Yakamata ku Sani Dangane da Kasar Nijar

Takaitaccen Tarihin Jamhoriyar Kasar Niger: Abubuwan da Yakamata ku Sani Dangane da Kasar Nijar

Jamhuriyar Nijar ta samo sunan ta ne daga kogin Naija duk kuwa da cewa ba ta kusa da wata babban mashigin ruwa. Nijar na makwabtaka da Najeriya da Benin ta kudanci, Burkina Faso da Mali ta yammaci, Aljeriya da Libiya ta arewaci, sai kasar Chadi ta bangaren gabas.

Kodayake sai a cikin karni na goma sha tara ne Turawa kamar Mungo Park dan kasar Burtaniya, suka fara shiga can bangaren kogin Naija, to amma dai tun kafin wannan lokacin Faransa ke ta kokarin ganin ta mallaki Nijar, inda ta samu nasara a shekarar 1890.

A wannan lokaci Faransa ta na da gwamnonin dake tafiyar da harkokin dukkanin yankunan da ta mamaye a yammacin Afirka ciki harda Nijar, wadanda ke aiki karkashin babban gwamna, wanda ke zaune a Dakar na kasar Senegal.

Ranar goma sha takwas ga watan Disambar shekarar 1958, Niger ta zamo Jumhuriya mai cin gashin kanta a karkashin ikon Faransa.
Sannan a ranar uku ga watan Agusta na 1960, jamhuriyar Nijar ta samu 'yancin kai, wato shekaru hamsin da suka wuce.

Kalubale

Jamhuriyar Nijar ta yi fama da juyin mulki daga sojoji daban daban wadanda suka mamaye madafen iko a kasar bayan ta samu 'yancin kai.
Kasar wacce ke fama da matsanancin fari, na fadi-tashin ciyar da jama'arta.

Babban abin da take fitarwa dai shi ne ma'adanin Uranium wanda shi ma a shekarun baya ya fuskanci rashin tabbacin farashi, yayin da kwararowar hamada ke barazana ga aikin noma.

Amma a gefe guda kasar na fatan fara hako man fetur wanda ka iya bunkasa tattalin arzikinta.

Bayan samun 'yancin kai, kasar ta fuskanci mummunan fari wanda ya lalata albarkatun noma.

Kasar dai ba ta da wani tsarin ilimin Firamare na azo a gani, abin da ya sa take cikin jerin kasashen da ke fama da rashin ingantaccen ilimi a duniya.

Harkar lafiya ma ba ta da kyau sosai, kuma akwai yaduwar cututtuka a ko'ina cikin kasar.

A lokuta da dama kasar ta yi fama da boren 'yan tawayen Abzinawa a Arewacin kasar.
Sai dai a shekara ta 2009, gwamnati da 'yan tawayen sun sanya hannu kan yarjejeniyar samar da zaman lafiya a birnin Tripoli na kasar Libya.

Shugaban mulkin soji: Salou Djibo

An bayyana babban jami'in soji Salou Djibo, a matsayin shugaban gwamnatin sojin kasar, bayan da sojoji suka hambaras da gwamnatin shugaba Mamadou Tandja a watan Fabrairun shekara ta 2010.

Jami'an sojin sun yi alkawarin mayar da kasar kan tafarkin dimokradiyya, sannan suka nada Fira minista farars hula Dr Mahamadou Danda, a matsayin shugaban gwamnati.

Hukumomin sun kuma haramtawa kansu da kuma jami'an gwamnatin rikon kwariya, shiga harkokin zaben kasar.

Juyin mulkin ya sa Tarayyar Afrika ta dakatar da kasar daga kungiyar, sai dai kasashen duniya sun yi taka tsantsan wajen Allah wadai da matakin da sojojin suka dauka, inda suka neme su da su maida kasar kan tafarkin dimokradiyya.

An haifi shugaba Janar Salou Djibo a shekarar 1965 a Arewacin yankin Tillaberi.

Ya samu horon soji a kasashen Ivory Cost da China da Morocco, sannan ya yi aiki da tawagar sojin kasar da ta yi aikin kiyaye zaman lafiya karkashin Majalisar Dinkin Duniya a kasashen Ivory Cost da jamhuriyar Congo.

Kafafen yada labarai

Gwamnati ce ke da mallakin kusan baki dayan kafafen yada labaran kasar, sai dai a 'yan shekarun nan an samu karuwar kafafen yada labarai masu zaman kansu.

Kafar Rediyo ita ce hanya mafi sauki da girma ta samun labarai a Nijar, akwai kuma jaridu na gwamnati da masu zaman kansu.

Gidan Radiyon Faransa na watsa shirinsa ta tashar FM a biranen Yamai da Maradi da kuma Zindar. Haka kuma ana kama BBC a zangon FM a gidajen rediyo masu zaman kansu da dama.

Akwai kuma masu amfani da hanyar sadarwa ta Intanet kimanin dubu tamanin a watan Yuni na shekara ta 2009.

Adadin jama'a

Kidayar jama'ar da aka gudanar a shekara ta 2009 a Nijar, ta nuna cewa yawan jama'ar kasar ya haura miliyan goma sha biyar.

Kidayar ta kuma nuwa cewa kashi tamanin da daya cikin dari na jama'ar kasar na zaune a yankunan karkara ne. Duk da arzikin albarkatun kasar da Allah ya yiwa Nijar, kimanin kashi sittin da biyar cikin dari na jama'ar kasar na rayuwa kan kasa da dalar Amurka daya, kwatankwacin kudin CFA 530 a rana (Watch Fluctuation na canji dala).

Batun cin hanci da rashawa da ake zargin shugabannin kasar na yi na taka rawar gani a halin talaucin da kasar Nijar ke ci gaba da fuskanta.

Fannin ilimi

A Jumhuriyar Nijar, tilas ne a ba kowanne yaro mace ko namiji mai shekaru shidda ilimin Firamare. Sai dai kuma yaran da ake sawa a makarantun Firamaren ba su da yawa musaman ma dai 'ya 'ya mata. kimanin kashi sittin cikin dari na yaran da suke kammala aji shida a Firamare maza ne, inda a yawancin lokuta ake tura yaran aiki a maimakon zuwa makaranta, musamman a lokutan damina.
Haka kuma akwai yaran makiyaya wadanda ba su da takamaiman matsuguni, ballantana makarantu.

Fannin Lafiya

Bangaren kiwon lafiya na da matukar rauni a jamhuriyar Nijar, dalilin da ya sa kasar take kan gaba cikin jerin kasashen da aka fi samun yawan mutuwar kananan yara a kasashen da ke makwabtaka da ita, musamman sabili da rashin ingantaccen abinci mai gina jiki da yaran ba sa samu.

A cewar kungiyar kare kananan yara ta Save the Children, Nijar ita ta fi kowace kasa a duniya yawan mace- macen kananan yara.
Har ila yau kasar na fama da yawan mutuwar mata masu juna biyu lokacin haihuwa.

Zirga zirga

Batun zirga- zirga na da muhimmancin gaske ga tattalin arzikin Nijar, inda hamada da manyan tsaunuka suka rarraba yankunan kasar musamman ta Arewaci.

Tun asali, babbar hanyar zirga- zirga a Nijar ita ce ta rakuma da wasu dabbobi ko bisashe kuma a wasu wuraren kamar kudanci da yammaci a kan yi amfani da 'yan abubuwan da ake da su ta ruwa da ba su da yawa.

Kuma hakan bai sauya ba ko lokacin mulkin Turawa. Har yanzu dai babu hanyar dogo ko jirgin kasa kuma ko kwalta babu a titunan da ake da su a lokacin mulkin Turawa.

Bayan da kasar ta samu 'yancin kai, sannu a hankali an samu manyan tituna da ake yawan zirga -zirga ta kananan motoci ko tasi, safa safa da manyan motocin daukar kaya.

Babban filin jirgin saman kasar shi ne na Diori Hammani dake a birnin Niamey. Akwai kuma wasu manyan filayen jirgin saman a Agadez da Zinder.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: BBC HAUSA

Thursday, 29 November 2018

Karanta Kaji: Kadan Daga Cikin Illolin Shan Taba Sigari Ga Lafiyar Dan Adam

Karanta Kaji: Kadan Daga Cikin Illolin Shan Taba Sigari Ga Lafiyar Dan Adam

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN-ƘAI. SALATI DA AMINCI SU TABBATA BISA ANNABIN DA BAI TA'BA SAƁO BA. DA IYALANSA DA SAHABBANSA DA DUKKAN BAYIN ALLAH NAGARI.

Rubutawa: Zauren Fiqhu

MECECE TABA SIGARI?

Ita dai taba sigari, ana samunta ne daga tsiron TOBACCO, wanda tarihi ya nuna cewa turawan Maxico da Spain sun kasance suna nomawa tun kusa Shekaru dubu kafin haihuwar Annabi Eisa (as) - wato 100 BC.
Taba Sigari ta shigo Qasar Amurka ne ta hanyar wani bature mai suna Christopher Colombus.

Kuma ta shigo Kasashen Africa ne ta hanyar turawa 'yan Mulkin Mallaka, da kuma 'Yan kasuwa.

Sun shigo da ita tun suna bayarwa amatsayin abun ciniki, suna karbar abubuwa irin namu na Africa, har zuwa lokacin da suka zama 'Yan Mulkin mallaka suka Kwace gonaki da filayen bakaken fata, suka fara nomata suna sayarwa kuma suna tafiya da ita zuwa Kasashensu.

HANYOYIN AMFANI DA ITA.

Mutanen wancan zamanin sun kasance suna Tauna ganyenta ne suna hadiyar yawun, daga baya kuma suka fara Sanya busashen ganyenta acikin Lofe (pipe) suna Zuka.

Daga baya kuma sai turawa suka Qirkiro wata sabuwar hanyar, suna Murza busashen ganyen tobacco suna sanyawa cikin takardun da aka nannade, wannan ita ake kira Sigari.

Daga baya kuma acikin 'yan shekarun nan sun bullo da wani sabon salo, suna sanya mata wasu sinadaran da suke sanya mata Qamshi irin na 'Ya'yan itace kamar Mangoro ko Strawberry ko Apple da sauransu. Wannan shi ake kira SHISHA.

ILLOLIN DA TAKE HAIFARWA

Illolin taba ga lafiyar 'Dan Adam ba zasu lissafu ba, sai dai mu gutsuro kadan daga cikin abinda bincike ya tabbatar kamar haka:

CIBIYAR BINCIKEN CUTUTTUKA TA KASAR AMURKA (CDC) TACE:

1. Shan taba Sigari yana sanadiyyar mutuwar Matasa sama da mutum 480,000 (dubu dari hudu da tamanin) duk shekara. Akasar Amurka kadai.

2. Sama da mutane MILIYAN SHA-SHIDA (16,000,000) ne suke fama da cututtuka daban daban wadanda suke da alaka da shan taba Sigari.

3. Anyi kiyasin cewa sama da mutane miliyon 88 ne suke cutuwa ta dalilin Sigarin da Waninsu yake sha. Kuma Mutane Miliyon 41 ne suka rasu ta dalilin shaqar hayakin da masu shan taba suke hura musu.

4. Sigari ita ce sanadiyyar kashi 90 (90%) na cututtukan Sankarar hunhu mai saurin Kisa (Lung Cancer).

Kuma ita ce sanadiyyar kashi 'daya cikin uku (33%) na duk wata cutar Daji (Cancer) wacce take damun 'yan Adam.

Misali akwai Mouth Ulcer, Cadio-Vascular diseases, da sauransu.

5. Tobacco ita ce sanadiyyar cuttuka masu kama Qirjin 'Dan Adam, kuma masu saurin kisa. Irinsu:

Chronic Bronchitis.
Emphysema.
Aneurism.
Vascular Disease.
Leukemia.
Cataract.
Pneumonea.

Mata masu ciki idan suna shan Sigari akwai yiwuwar Jaririn da yake cikinsu ya kamu da cutar nan ta Asthma. Ko kuma suyi bari, ko kuma su haifi yaron acikin wani irin yanayi.

6. Sigari tana shiga hanyoyin jini, tana gurbatashi, tana toshe ƙofofin da zuciya take harba jini ajikin 'Dan Adam..

ABUBUWAN CUTARWAN DA TAKE KUNSHE DASU:

Acetone.
Acetic Acid.
Ammonia.
Arsenic: wani abu ne wanda ake hada maganin bera dashi.
Benzane.
Butane.
Cadmium : wani irin acid ne.
Carbon Monoxide.
Formaldehyde.
Hexamine.
Lead.
Napthalene.
Methanol.
NICOTINE: Gubar da ake hada maganin Qwari dashi.
TAR: abinda ake zubawa akan tituna (Kwal-ta)
TOLUENE.

Duk wadannan abubuwan akwaisu acikin taba sigari. Kuma kowannensu ko shi kadai aka bari, zai iya hallakar da 'Dan Adam.

ILLOLINTA TA FUSKAR ADDINI

Illolinta ta fuskar addini suna da yawa. Daga ciki akwai:

1. Almubazzaranci ne. Tunda batta amfanar da komai ga jikin 'Dan Adam. kuma Allah yace "Hakika Almubazzarai sun kasance 'Yan uwan Shaitan ne. Shi kuwa Shaitan ya riga ya kafurce ma Ubangijinsa".

2. Tana cutar da lafiyar masu shanta. Allah yana cewa: "Kar ku jefa Hannayenku cikin hallaka".

3. Tana cutar da wadansu: Manzon Allah (saww) ya lissafa Mai cutar da Makobcinsa acikin mutanen da ba zasu shiga Aljannah ba.

Wannan hoto da ke ƙasa misali ne na huhun wanda ba ya shan taba da wanda yake sha.

Hoto daga Dr Hinal

Wannan tunatarwa ce ga dukkan masu hankali. Ku hana kanku, ku hana 'yan uwanku da abokanku shan Sigari.

ALLAaH YA SAWAƘE!

Amin Summa Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Zauren Fiqhu

Sunday, 28 October 2018

KARANTA KAJI: JIHOHI GUDA BIYU A KASAR NIGERIA BAZASU TAƁA ZAUNAWA LAFIYA BA

KARANTA KAJI: JIHOHI GUDA BIYU A KASAR NIGERIA BAZASU TAƁA ZAUNAWA LAFIYA BA

Wadannan jahohi bazasu taba samun zaman lafiya ba har sai sun dawo ga tirbar da aka san su da ita.

1. JAHAR BORNO

2. JAHAR ZAMFARA.

Marubuci: Mansur Musa Mancy Wanzamai

Wadannan jahohi bazasu taba samun zaman lafiya ba har sai sun dawo ga tirbar da aka san su da ita.

jahar borno, duk Africa idan akazo fannin sanin ilimin qur'ani basuda na biu. Allah ya azurtasu da masana littafin sa mai tsalki amma sai suka maida qur'anin Allah abun yin sihiri da tsibbace-tsibbace, tare da amfani da ayoyin ubangiji ta mummunar hanya.

Shin kuna ganin Allah zai barsu haka, ba tare da ya jarabce su da ukubar sa ba !!!?

Haka kuma, Zamfara, Wadda akeyiwa kirari da "Noma da shari'a sune tunkahon mu," itace jaha ta farko a duk Africa data nunawa duniya cewa tayi alkawalin tafiyar da dukkanin lamurran ta abisa tsarin shariar musulunci.

Aka kafa shari'a, ko kuma ince aka jaddadata, amma daga bisani sai muka yaudari kawunan mu, mukayi watsi da shari'ar nan, harma munayiwa Allah izgikl, muka dauki kalamar "shari'a" wata kalma ta yaudarar al'umma.

Yau jahar zamfara takai matakin da duk wani kalar zunubi da aka aikatawa a Nigeria zamfara ta lunka shi.

Shin kuna ginin Allah zai kyale jahar zamfara ba tare da ya addabe mu da musibu kala-kala ba !!!?.

Ina mai rantsuwa da Allah akan cewa, wallahi Idan da zaa kawo dukkanin Africa a jahohin zamfara da borno bazasu iya kawar da wadannnan musibu da suka addabe mu ba har sai mun farfado daga barcin da mukeyi.

Gwamnati bazata iya kawo muna zaman lafiya ba, har sai mun dawo ga Allah.

Yazama dole ga malamai suyiwa gwamnati bore domin dawo da martabar Shari'a a jahar zamfara.

Yazama dole malaman Nigeria su yaki matsibbatan da suka addabi jahar borno idan har anson zaman lafiya ya wanzu a kasar mu Nigeria.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

Sunday, 21 October 2018

KARANTA KAJI: TAKAITACCEN TARIHIN DAURA A AREWACIN NIGERIA

KARANTA KAJI: TAKAITACCEN TARIHIN DAURA A AREWACIN NIGERIA

Tsohon Littafin tarihi na masarautar Daura da ake masa laƙabi da suna Girgam kamar dai sauran littattafan tarihin yawa-yawan masarautu, ya ruwaito cewar tun a wajajen shekaru dubu biyu kafin haihuwar Annabi Isah A.S wasu mutane ƙarƙashin jagorancin shugabansu mai suna Najib (Wasu sunce Nimroid ko Namarudu sunansa) suka yo hijira daga ƙasar su ta haihuwa Kan'ana tare da riskar inda ƙasar Daura take a yanzu.

Marubuci: Sadiq Tukur Gwarzo

Babu takamaen dalilin tasowar su, amma dai ance akan hanyar su ta tafiya, sun yada zango a tsohuwar Misira tsawon wani lokaci har kuma daga bisani wasu Misirawan na dauri suka shigo cikinsu akayi hijirar tare dasu.

Ance kuma da suka baro Misira sai suka shigo cikin ƙasar Libya, inda suka sauka a birnin Tarabulus, a zamanin da wani Sarki mai suna Abdurdaar ke mulkinta har ya so ya mallake wannan runduna amma bai samu nasara ba, daga ƙarshe shi Najib ya cigaba da tafiya da mutanensa har suka riski wani wuri da ake kira Tsohon birni, inda suka fara kafin birnin Daura kafin su koma sabuwar Daura.

Akwai ƙarancin sani matuƙa game da kafuwar daura ko kuma tsawon lokacin da tayi tana sharafi.

Marubuci Zakariyya Kabo ya kawo hujjojin cewa Daurawa misirawa ne da suka zo daga ƙasar su ta misira a littafinsa mai Suna 'Gamsasshen Tarihin Hausawa'.

Ga kaɗan daga hujjojinsa akan haka:-

1. Da akwai wani takobi mai rubutu ajikinsa irin na mazauna kasar misira ada can wanda koda turawa suka zo sai da suka ce wannan takobin babu masu irinsa sai misirawa. Kuma ko yanzu kaje Daura ana iya ɗauko maka shi ka gani.

2. Yanayin tsarin gine-ginen fadar Daura ɗaya ne dana misirawan-da. Zakaga anyi soro, sannan katangun gida masu kaurin Gaske. Akan kuma yi manyan turaku da babban fili a matsayin tsakar gida da manyan zaurukan hutawar sarki.

3. Tamburan da ake zanawa a bangwayen gidan sarauta na Daura.

Haka shima Marubuci Maje Ahmad Gwangwazo ya tafi akan cewa tsoffin mazauna Daura Mangawa ne waɗanda basa jin Hausa, don haka koda Bagauda ya riski Kano sai daya shafe aƙalla shekaru biyu yana Koyon harshen Hausa na mazauna Kano.

Akwai kuma masu ganin cewa hijira biyu ko uku akayi daga can kan'ana zuwa Daura. Inda suka ce a hijira ta farko, Najib ne ya jagorance ta. Amma a hijira ta biyu, wata jaruma da ake kira Daurama ce ta jagorance ta. Kuma daga sunan tane aka laƙabawa birnin suna Daura, har kuma aka samu cewa an shafe tsawon lokaci mata ne ke jagorantarsa.

Ga sunayen Sarakunan farko da aka samu sun mulki Daura tun tsawon lokaci da ya gabata:-

1. Kufuru
2. Ginu
3. Yakumo
4. Yakunya
5. Wanzamu
6. Yanbamu
7. Gizir-gizir
8. Inna Gari
9. Daurama
10. Ga-wata
11. Shatu
12. Fatatuma
13. Sai Da mata
14. Ja Mata
15. Ha-Ma
16. Sha-wata
17. Daurama II (wadda alokacinta ake tsammanin Bayajidda yazo Daura).

An samu cewa kusan dukkan waɗannan sarakuna mataye ne, ana kiransu da suna 'Kabaras ' fassararsa shine Magajiya da hausa. Watau wadda tayi gadon mulki kenan.

Haka kuma, akwai maganganu na tarihi dake nuna cewar an samu ɓullar Shugabanni mataye masu laƙabin 'Kabara' a wasu masarautu na ƙasar Mali, da Isra'ila.

Amma dai babu wanda ya tabbatar da wata alaƙa data kasance tsakaninsu da waɗannan Kabarori na Daura duk da cewar akwai hasashen yanayin bautar da akace Kabarorin sunyi yafi kamanceceniya shigen wadda aka taɓa samu anyi a Isra'ila.

Zuwan Bayajidda akafi labartawa a matsayin tarihin Hausa da Hausawa, amma a zahiri, labarai sun nuna cewar Bayajidda ya riski Daura ne a zamanin da Sarauniya Daurama Shawarata ke mulki, ita kuwa ana ganin itace sarauniya ta goma sha bakwai a tarihin mulkin Daura.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

Monday, 1 October 2018

KARANTA KAJI: SHEKARU 58 DA SAMUN 'YANCIN KAN NAJERIYA CI GABA KO KOMA BAYA?

KARANTA KAJI: SHEKARU 58 DA SAMUN 'YANCIN KAN NAJERIYA CI GABA KO KOMA BAYA?

Tun a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1960 ne, Najeriya ta samu 'yancin kanta daga turawan mulkin mallaka na Ingila, wanda hakan ke nuni da cewa kasar ta cika shekaru 58 da samun wancan 'yanci.

Marubuci: Abba Ahmad Gwammaja

Kasar kuma ita ce kasa mafi yawan jama'a a yankin nahiyar Afrika, wadda ake kiyasin cewa tana da jama'ar da suka doshi miliyan 200 (shi yasa ma ake mata lakabi da "Giwar Afrika" ko kuma "Giant of Africa" a turance), kuma daya daga cikin kasashe masu arzikin man fetur a duniya baki daya.

Cikin wadannan shekaru, kasar tayi shugabanni daban-daban har guda 14.

Sai dai kuma a cikin wadannan shekaru babu yadda za'ayi ace kasar bata samu wani ci gaba ba ko k'ak'a yake, haka nan babu yadda za'ayi ace ba'a samu koma baya ba ko k'ak'a.

Amma ana yin hukunci ne da abinda yafi rinjaye.

Dukkanin wata kasa da ta samu ci gaba a duniya ya samu ne ta 6angaren gwamnati da kuma jama'ar gari.

Inda a 6angaren gwamnati ake duba wasu abubuwa kamar haka:

1. Harkar lafiya (Health): Farkon abinda kowanne dan kasa yake bukata shine a samar masa da ingantattun asibitoci, magunguna da kuma kwararrun likitoci, dan kuwa da zarar an haifi jariri a gida ko a asibiti, lafiyarsa da ta mahaifiyarsa ita ce abu na farko da za'a fara tambaya, bayan anyi masa wasu 'yan gwaje-gwaje don a tabbatar da cewar lafiya kalau aka haifeshi babu wata cuta a jikinsa ko kuma wani nak'asu.

Sai kuma rigakafin da za'a ringa kaishi asibiti ana yi masa duk bayan wani lokaci, har izuwa wani wa'adi.

2. Ilmi (Education): Da zarar yaro yakai shekaru 3-4 kuma, sai gwamnati tayi iyakacin iyawarta don ta fara shigar dashi a tsarinta na ilmi mai nagarta, kuma kyauta tun daga matakin Firamare har zuwa makarantar gaba da Sakandire, inda zai fara da ECCE, kamar yadda sashe na 18 na kundin tsarin mulkin kasa yayi umarni.
Inda zata samar masa da kyawawan tsaruka wanda suka hada da: Gine-ginen makarantu, kwararrun Malamai, da kuma isassun kayyakin koyo da koyarwa.

3. Aikin yi ko sana'a (Job or Occupation): Da zarar kowanne dan kasa ya samu isashshiyar lafiya da nagartaccen ilmi, to kuwa abu na gaba da yake bukata shine sana'a ko kuma aikin yi, wanda da safe idan ya tashi yasan inda zai nufa, yayinda da yammaci kuwa zai koma gida domin ya huta, kafin gobe da safe ya nufi gurin aikinsa.

Kuma hakan ce zata saka ya dogara da kansa, tare da wadatuwa da dan abinda zai kai bakin salati shi da iyalansa, kuma ya biya wasu bukatunsa na yau da kullum, har ma ya taimakawa wasu makusantansa.
Kaga kenan yayi bankwana da zaman banza, ballantana har takaishi ga aikata wasu muggan laifuka, tunda a kullum idan ya tashi da safe yasan inda zai dosa.

4. Tsaro (Secuirity): Da zarar kowanne dan kasa ya samu isashshiyar lafiya, nagartaccen ilmi da kuma aikin yi ko sana'a, to kudi kadan gwamnati zata kashe wajen samar masa da tsaro, dan kuwa a kullum zai kasance bashi da isashen lokaci nasa na kansa, ballantana har takai ga ya tada husuma ko kuma ya aikata wani mugun laifi.

Zaman banza da rashin aikin yi shine jagoran aikata dukkanin wasu manyan laifuka a duniya baki daya, kaga kenan da zarar al'umma ta wadatu da aikin yi, to kuwa za'a samu karancin aikata laifuka, tada zaune tsaye da kuma rashin zaman lafiya.

Kuma babu wata kasa a duniya da zata ci gaba matukar babu zaman lafiya a cikinta.

5. Kayayyakin more rayuwa (Basic Aminities/
Infrastructure): Da zarar 'yan kasa sun wadatu da wadancan abubuwa guda 4 na sama, sai kuma gwamnati ta mayar da hankali wajen sama musu kayayyakin more rayuwa, wadanda suka hada da:

a. Wutar lantarki (Electricity).

b. Ruwan sha (Water Supply).

c. Hanyoyin Sufurin kasa, na ruwa da na sama (Land Transpotation, Water Transpotation and Air Transportation).

d. Hanyoyin Sadarwa (Telecommunication).

e. Kafafen yada labarai (Media).

f. Kayayyakin kwasar shara (Refuse disposal).

g. Masana'antu (Industries).

h. Noma da albarkatun kasa (Farming activities and Mineral Resources).

Da makamantansu.....

Inda a 6angare guda kuma, jama'ar gari ana son su kasance 'yan kasa nagari masu bin doka da oda, marasa son fitina, masu hadin kai da son ci gaban kasar, tare da 6ullo da dukkanin wasu tsaruka da zasu taimakawa kasar taci gaba, kuma su gujewa dukkanin wadansu abubuwa da zasu jawo zubewar mutuncinsu da kuma kasarsu a ko ina suka samu kansu, haka nan su guji lalata kayayyakin gwamnati.

Don kuwa mutum daya yana iya jawowa kasarsu 6acin suna, haka kuma zai iya daga sunan kasarsu a idon duniya.

Sannan kuma shin sun wadatu da wadancan abubuwa da ake bukatar gwamnatocin su samar musu dashi ko kuma basu wadatu ba?

Wadannan abubuwan da makamantansu sune ma'aunin da ake amfani dashi wajen gane cewa kasa ta samu ci gaba ko kuma koma baya a tsahon wani lokaci.

Saboda haka sai mu auna mu gani, a tsahon wadannan shekaru 58 ci gaba muka samu ko kuma koma baya?

Ku ci gaba da Kasancewa da mu domin samun Cikakkun Bayanai masu gamsarwa.

Happy independenceday

Nigeria@58

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng a duk inda ku Kasance a faɗin Duniya domin samun sahihan Tarihi Daban-Daban a faɗin Duniya.

KARANTA KAJI: TARIHIN ASALIN ZAMFARAWA