Saturday, 25 November 2017




Na fada wa Buhari halin da talakawa suke ciki – Sheikh Bala Lau

Home Na fada wa Buhari halin da talakawa suke ciki – Sheikh Bala Lau

Anonymous

Ku Tura A Social Media



Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa
Iqamatul Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala
Lau, ya shaida wa BBC dalilin da ya kai su fadar
shugaban Najeriya.
A farkon watan nan ne wadansu malaman addinin
Musulunci a kasar suka kai wa Shugaban Najeriya
Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.
Sheikh Bala Lau ya ce dalilin zuwansu fadar bai
wuce batun cewa shugaban ya kwashe lokaci mai
tsawo bai sadu da malaman addinin ba, tun gabanin
ya fara jinya a farkon shekarar nan.
Malamin ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo
mana ziyara a ofishinmu na Landan ranar Alhamis
tare da rakiyar Sheikh Kabiru Gombe.
"Ba kawai malunma na addinin Musulunci shugaban
ya gani ba. A'a har da ma malaman addinin Kirista
ya gana da su a lokacin," in ji shi.
Ya ci gaba da cewa: "Babu shakka mun shaida
masa halin da talakawa suke ciki har ayoyin
Al'kur'ani sai da na karanta masa."
Har ila yau malamin ya ce sun bukaci shugaban da
ya rika kawo sauki a cikin shugabancinsa.
Kuma ya ce shugaban ya ba su tabbacin aiki da
shawarwarin da suka ba shi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: