Wani abu da ya ke yawan damun masu
amfani da wayoyin hannu musamman
irin wadannan wayoyin komai da
ruwanki wato Smartphones shi ne
yawan yin zafi kamar zata kona hannu
ko kuma dimi da mutum bai samun
kwanciyar hankali da shi. Wani lokaci a
wurin maza sai su ce idan suka saka ta
a cikin aljihunsu sai ta dau zafi, wani
lokaci ma sai da ka dauko ka duba
kawai sai ka ga ai ta mutu saboda da
irin wannan zafi.
A wannan darasi da zamu yi zamu fada
muku abubuwan da ke kawo waya ta
rika yin zafi da kuma hanyoyin da zamu
kiyaye domin mu hana ita wannan
wayar yin zafi.
Masu yawan sauraron labarai sun sami
labarin kiranye da janye wayar
kamfanin Samsong suka yi a ‘yan
kwanakin baya kasancewar sabuwar
wayar da ta shigo kasuwa haka nan
kawai sai ta kama da wuta saboda
matsala da aka samu wurin gina batirin
ta. Wannan ya sanya muka ga ya dace
muyi muku bayani game da irin zafin da
idan kaji wayarka tana yi ka gane
cewar akwai matsala.
Waya Na Yin Dumi
Baki ko sabon shigar amfani da wayoyin
smartphone su sani cewar irin wannan
wayar tana yi dumi wanda ya sha
banban da irin kananan wayoyin da
suke amfani da su a baya. Mu sani
smartphones kayan wutan lantarki ne,
saboda haka don kaji tayi dumi ka sani
ba wani matsala ba ne.
Amma kuma idan kaji tayi zafi wanda
kake jin tsoron zai iya lalata ta, ko
kuma ta yi zafin da kake jin tsoron za ta
iya fashewa ko ma ta la’anta masu
amfani da ita to lallai ka na inda ya
dace, domin abin da zamu tattauna ke
nan.
Duk da cewar mafi yawan abin da zan
fada sun fi karfi ga wayoyi masu amfani
da fasahar wayar Android domin kusan
su aka fi amfani da su a wannan nahiya
tamu ta Afirka musamman Najeriya ta
Arewa.
Ta wane wuri waya ke yin zafi?
Abu na farko da ya kamata mu fara
kiyayewa shi ne ta wani wuri wayar
take fara yin zafi? Duk da cewar nasan
ba kuwa ba ne zai iya lura ko kiyayewa
ba, amma dai zai iya yiwuwa ta batir ne
ko kuma
Monday, 6 November 2017
Author: Anonymous verified_user
0 Comments:
Post a Comment