- Ta yi wasika domin a sanyawa 'yar tata suna
- Gwamnati ta ji qan jaririyar
An sami jaririya Aishatu, a bola uwarta ta wullarta, ta kudundune a tsumma, inda ta bar wasika cewa zata dawo ta dauki 'yar tata idan ta tasa.
An amsa mata an kuma dauki 'yar, a hukumar hisba ta jihar ta Kabbi, sai dai gwamnati ma tace baza a barta a baya ba, inda yanzu matar gwamna, da Sanata daga yankin, suka bayyana cewa gwamnatin jihar zata dauki nauyin 'yar har muddin rayuwa.
Tun daga abinci da sutura har karatu da auren ta.
Ga dukkan alamu dai duk inda uwa da kakar wannan 'ya suke sai yanzu ne zasu fara kuka da da-na-sani na wannan aika aika da suka yi, wadda ta zame musu abin kunya ffiye da abin kunyar da a da suka aikata na cikin yarinyar.





0 Comments:
Post a Comment