- Hadiza Mohammed ta ce a cikin fina-finan su ana yin karatun alkur'ani kuma ana jan baki da fasarawa
- Da sannu mutane za su fahimce mu inji Hadiza Mohammed
Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Mohammad, ta ce yan fim din Hausa sun zama abun da Hausawa ke cewa dankali sha kushe.
Hadiza ta ce Allah yana kallon abun du suke yi, idan suna yin fim ne dan su bata tarbiyya ko kuma gyara da fadakarwa Allah ya sani.
Ta ce a cikin fina-finan da suke yi akawai karatun Al-kur’ani, ana jan baki kuma ana fasarawa, sannan ana cewa Allah yace, Annabi yace; shima duk wannan koyar da rashin tarbiyya ne inji Hadiza.
Hadiza ta bayyana hakan ne a lokacin da take amsa tambayoyi da BBC su ka mata akan zargin bata tarbiyyar al’umma da ake yiwa yan fim.
Ta kara da cewa: “Kun san mu dankali ne sha kushe, ana son mu kuma ana kushe mu. Amma haka za mu yi ta tafiya tun da sana’ar da Allah ya kaddara za mu yi kenan.
“Yakamata ayi hakuri da damu, saboda muma muna hakuri da masu kushe mu, amma da sannu za su fahimci mu. Nasan akwai wadanda suka fahimce a yanzu.”
0 Comments:
Post a Comment