Monday, 8 January 2018




Wata musulma, ba'amurkiya ta rungumi wanda ya kashe mata danta ta kumace ta yafemai: Jawabinta akwai sanyaya zuciya

Home Wata musulma, ba'amurkiya ta rungumi wanda ya kashe mata danta ta kumace ta yafemai: Jawabinta akwai sanyaya zuciya

Anonymous

Ku Tura A Social Media


Wannan wata baiwar Allahce musulma me suna Rukiye, 'yar kasar Amurka da wasu suka kashe mata danta, Sulaiman Ahmad haka kawai siddan, suka dauke kudin jikinshi da kuma abincin da ya siyowa matarshi.



Saidai wani abun birgewa daya faru a kotu da akazo gurin shari'ar kisan dan na Rukiye shine, tana ganin daya daga cikin wadanda suka kashe dan nata( wanda a lokacin da sukayi kisan shekarunshi goma sha hudu) sai ta tashi ta rungumeshi ta kuma rungumi mahaifiyarshi, taje ta gaisa da dukkan 'yan uwanshi.


Rukiye tayi jawabi a kotun inda tace bata tsani wanda ya kashe mata dan nataba, karamin yarone, kuma ba zata taba tsanarshiba, tace ba halin mu(Musulmi na gari bane) tsanar mutum, a koda yaushe muna nunawa mutum tausayi dan haka ta yafe mai, bataso a lasheshi dalilin kashe danta da yayi, Allah dama ya riga ya kaddaro mutuwar dan nata bazai wuce wannan ranar ba saiya mutu, kuma kashe shi wannan yaron bazai dawo mata da rayuwar dantaba, saboda haka babu wani alheri a cikin ramuwar gayya, ta yafe mishi.


Wannan yana kunshene a cikin wani bidiyo wanda aka dauka lokacin da matar take jawabi a korun, kuma bidiyon yayita yawo a yanar gizo anata yabawa matar da irin wannan jarumta data nuna. Muna fatan Allah ya kara daukaka musulunci da musulmi, ya jikan sulaiman da dukkan musulmi da suka rigamu gidan gaskiya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: