Dan dai na Gwamnan na farko mai suna Aham Brendan Okorocha an bayyana cewa ya kwanta rashin lafiya kafin daga baya a fita da shi zuwa kasar waje domin samun kulawa ta musamman.
ArewaTop.com dai ta samu kishin-kishin din hakan ne a jiya Lahadi a garin Uburu, jihar Ebonyi yayin wani taron siyasa da aka gabatar inda aka bayyana dalilin rashin zuwan shugaban jam'iyyar APC na rashin ruwan sa taron da rashin lafiyar dan.
A wani labarin kuma, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce 'yan Nigeria suna da gajen hakuri na son rayuwar su ta inganta cikin gaggawa fiye da karfi da arzikin da kasar ke da shi.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi kan bukin sabuwar shekarar 2018.
0 Comments:
Post a Comment