Amurka za ta fallasa Iran
Amurka ta ce za ta gabatar da gyauron makamai waɗanda ta ce Iran ce ta samar wa ƴan-tawayen Huthi na Yemen.
Jakadiyar Amurka a majalisar ɗinkin duniya Nikkey Haley za ta nuna shaidar ga wakilan ƙasashen kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, a ƙoƙarin da Amurka ke yi na ganin majalisar ɗinkin duniya ta ƙara takura wa Iran.
Watanni da dama ke nan tun bayan da ƙasar ta Amurka ke bibiyar majalisar ɗinkin duniya wajen ganin ta hukunta Iran, inda har Amurka ɗin ta yi barazanar ficewa daga yarjejeniyar jingine shirin makamin nukila da aka ƙulla da Iran.
Tuni dai Iran ta musanta cewa tana samar wa ƴan-tawayen Huthi makamai, sannan ta bayyana shirin Amurka ɗin a matsayin na bogi.
Sunday, 4 February 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
In the face of public embarrassment, Woolworths has withdraw from sale a lookalike product a Cape Town entrepreneur says it stoleIn the face of public embarrassment,Woolworths ha
KALLI YADDA AKE YIN TSERE ASARARIN SAMA NIYYAKalli yadda Usain Bolt ya yi tsere a sararinsaman
News about flailas resultWhen Will Flailas Release Results For the 2018 Se
Myschool CBT Challenge Season 5 - Cash Prize Of N200,000 To Be Won! We are pleased to announce the Myschool CBT Chall
YANDA AKAYI JANA IZAR MARIGANYI SHEHU SHAGARIKaranta bayanai da labarai game da jana'izar tsoh
SHUGABA MUHAMMADU BUHARI ZAIYI JAWABI GA TA KWARORINSA NA DUNIYYA Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi gatakwaror
0 Comments:
Post a Comment