Kaduna: Zaki ya kufce daga gidan Zoo
A ranar Asabar mutane da ke zuwa filin shakatawa na Gamji Gate a Kaduna suka tsallake rijiya da baya bayan da wani zaki ya kufce daga inda ake tsare da shi.
Majiya daga filin shakatawar ta Gamji Gate ta shaida wa wakilin BBC cewa Zakin ya kufce ne yayin da daya daga cikin masu kula da shi ke bashi abinci.
Rahotanni sun ce Zakin ya yayyaga shi, ya kuma sami nasarar ficewa daga wurin da ake tsare da shi.
An yi ta gudu a filin na Gamji bayan da masu shakatawa su ka tsinkayi Zakin.
Wadanda suka shaida lamarin da idonsu sun kuma bayyana wa BBC cewa Zakin da kan sa ya koma cikin inda aka killace shi ba tare da ya kassara wani mutum ba.
Filin shakatawa na Gamji a Kaduna na da karamin wurin ajiye namun daji wato, Zoo kuma akwai Zaki, da Jimina, da wasu Birai, Bareyi da kuma Kuraye.
Akan zargi masu killace irin wadannan namun daji da barin su cikin yunwa, abinda watakila ya sa su ke tunzura har su yi kokarin kufcewa.
Wakilin BBC, Nura Ringin ya ce, "Ranar Laraba da na shiga Gamji Gate babu shakka na ji Zaki na ta gunji."
Sunday, 4 February 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Kasashen Najeriya da Syria da Afghanistan, daIraq
Electoral bill: Senate reportedly plotting to override President Buhari[post by samaila umar lameedo] Electoral bill: Se
MUTUMIN DA YAFI KOWA YAWAN DA RIYYA ADUNIYYAGa mutumin da ya fi kowa yawan dariya aduniya. Bi
About 10,000 light years away from Earth, a black hole is engaged in a stellar feastAbout 10,000 light years away from Earth, ablack
KALLI YADDA AKE YIN TSERE ASARARIN SAMA NIYYAKalli yadda Usain Bolt ya yi tsere a sararinsaman
A NIGERIA MASU FASHI ATEKU SUN SACE MA AIKATA12 NA WANNI JIRGIN RUWAN MALLAKAR KASAR SWITZLANDA Nigeria masu fashi a teku sun sace ma'aikata12
0 Comments:
Post a Comment