Mujallar Fim Ta Wannan Watan Ta :Gwagwarmayar Da Jaruma Sadiya Adam Da Angon Ta Sanusi Ahmad Su ka Shiga kafin Iyayen Su, Su kyale su Yi Aure
1. Hira da Maryam Isah (Ceeter) a kan ci-gaban da ta samu a Kannywood tun bayan mutuwar auren ta.
2. Gwagwarmayar da jaruma Sadiya Adam da angon ta Sanusi Ahmad su ka shiga kafin iyayen su su kyale su su yi aure a makon jiya.
3. Ni yanzu tsoron aure na ke ji, inji Fati KK. Hira da jarumar a kan halin da ta ke ciki bayan mijin ta ya sake ta da 'ya'ya biyu kwanan nan. Shin za ta dawo harkar fim ne ko yaya?
4. Labarin rasuwar wasu 'yan fim guda biyu.
5. Yadda jarumi Bello Mohammed Bello (General BMB) ya iza wutar rikicin 'na fi ka, ni ma na fi ka' wanda ake yi tsakanin Ali Nuhu da Adam A. Zango.
6. Furodusa Sani Sule Katsina inuwar giginya ne, inji jarumi Aminu A. Daggash wanda ya yi aure a makon jiya.
7. Yadda aka bata wa mutane rai a taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya da aka yi a Katsina.
8. Akwai sauran labarai masu gamsarwa a cikin wannan mujallar.
0 Comments:
Post a Comment