Wednesday, 4 April 2018




Sarkin Kano na bogi zai yi wata 36 a gidan yari

Home Sarkin Kano na bogi zai yi wata 36 a gidan yari

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Sarkin Kano na bogi zai yi wata 36 a gidan yari


An kama dalibi Sultan Bello da laifin yaudarar mutane a kafar sada zumunta da sunan sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu

Dalibi Sultan Bello wanda ke boye kama da sunan sarkin Kano Muhammad Sanusi a kafar sada zumunta ya samu hukuncin tsarewa a gidan yari na tsawon wata 36.

A zaman da aka yi a kotun majistere dake nan Kano ranar, Litinin 26 ga watan maris mai laifin ya samu hukuncin bayan karar da aka shigar kan sa.

An kama shi da laifufuka uku wanda ya hada da shigar burtu da yaudara da bata suna.

Mai shari'a Hassan Ahmad ya zarce hukuncin bayan wanda ake tuhuma ya nemi rangwami kan laifin da ya aikata.
Jami'in dan sanda da ya gurfanar dashi gaban kotu ya shaida cewa mai laifin ya bukaci kudi daga hannun jama'a ta hanyar yaudara da sunan mai martaban.

A cewar sufeto Haziel Ledapwa "Bello ya bukaci kudi wanda jumlar shi ya kai naira miliyan 1.85 (N1.85)

 N1.4 daga hannun wata Baraka Sani. Banda ita ya kuma bukaci kudade kamar haka:

N150,000 daga wani Sadiq Saflan
N50,000 daga Sadiq Sani
N50,000 daga Surajo Zakari
N150,000 daga Yahaya"
Bayan watanni da dama da yin bincike kan gano shi, jami'an tsaro suka samu nasarar garkame shi cikin watan febreru na 2018.

Tun kwanakin baya dai shi Mai martabar sarkin kano ya sanar cewa baya kawance a shafukan sada zumunta don haka jama'a su kiyaye.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: