Za A Nada Adam A. Zango Sarkin 'Yan Finafinan Hausa
Kungiyar masu kallon finanfinan Hausa ta kasa baki daya tana daf da baiwa jarumi Adam A. Zango sarautar 'yan fim din Hausa.
A yayin da RARIYA ta zanta da shugaban riko na kungiyar Fala M. Shareef don jin dalilin su na baiwa Adam Zango wannan sarauta, ya bayyana dalilin da ya sa za su ba Adam Zango sarautar ta kanywood kamar haka; don kasancewar sa mai hakuri, iliminsa mutuncinsa, kyautarsa, biyayyarsa, ibadarsa, yafiyarsa ida an yi masa laifi da kuma daukakarsa.
Sannan kuma mawaki ne, makadi ne,furodusa ne, darakta ne, edita ne, jarumi ne, dan rawa ne da dai sauransu.
Fala ya kuma kara da cewa wanan sarautar ba su bada ita dan kuntatawa wani ko wata ba sai dan shine wanda ya kamata a baiwa kuma dama can babu sarki a masana'antar fim.
riff ya ce "Wannan dalilin ne ya sa muka zauna dan tattaunawa akan wa ya kamata aba. Bayan mun yi haka sai muka ga shine wanda ya cancanta.
Sannan wannan sarautar ba mu muka ba shi ba Allah ne ya ba shi.
"Sannan kuma kar ku manta mu ma masu kallo muna da 'yanci akan masu shirya finafinan Hausa. Dalilina shine in ba mu ba za su yi ba saboda su suke shiryawa mu kuma muke siya.
Tuni har wasu masoyan Adam Zango suka shirya bikin taya shi murnar wannan sarauta da za a ba shi.
Inda masoyansa da dama suka halarci bikin cikin shigar sarauta da al'adu wanda aka gudanar a jihar Nasaarawa.
Masoyan na A. Zango sun kuma ce yadda aka ga sun yi a wurin taya murnar haka za su yi a ranar nadin sarautar.
Masoyan Zangon sun kuma kara da cewa daga yanzu ba za su kara bari ana cin zarafinsa da tozarta shi ba, inda suka yi barazanar cewa idan aka kara nuna masa bambanci a masana'antar fim za su dauki mataki.
Thursday, 5 April 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Rigima Ta Barke Tsakanin Teema Makamashi DaTsohuwar Jarumar Kannywood Fati Muhd Akan Wani Wai Shi Dino Malaye.Rigima Ta Barke Tsakanin Teema Makamashi DaTsohuw
Hotunan bikin Adam a zango tare da amaryarsa soffy.Hotunan bikin Adam a zango tare da amaryarsa soff
Kalli wasu kyawawan hotunan maryam yahaya na wannan makon. Kalli wasu kyawawan hotunan maryam yahaya na wann
An kara kwanaki na auren jarumi Adam a zango wanda auren nashi Ya kasance na 6.An kara kwanaki na auren jarumi Adam a zango wand
Saratu Gidado Na Nema Wa Tsohuwar Jaruma Bilkin R.K. Agajin Gaggawa.Saratu Gidado Na Nema Wa Tsohuwar Jaruma Bilkin R
mina Amal ta maka Hadiza Gabon Kotu saboda dukan data sa aka yi mata da cin zarafi. Amina Amal ta maka Hadiza Gabon Kotu saboda dukan
0 Comments:
Post a Comment