Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa uwargidan shugaban kasar Brazil, Marcela Temer, ta yi kukan kura ta tsunduma cikin wani tafki dake fadar shugaban kasar domin ceto karen ta da ta saba kiwon sa.
NAIJ.com ta fahimci cewa wannan lamari ya sanya batutuwa da musayar ra'ayoyi akan ta su suke ta kwaranya a kafofin watsa labarai da dandalan sada zumunta.
Fitacciyar uwargidan mai shekaru 34 a duniya da ta shahara da kyawun sura da kuma sifa ta tsunduma cikin tafkin ne bayan da karen ta mai sunan Picoly ya afka cikin sa yayin bibiyar wasu agwagi kuma ya gaza fitowa.
Wannan lamari mai ban mamaki gami da kamanceceniya ta wasan kwaikwayo ya afku ne a ranar 22 ga watan Afrilun da ya gabata, wanda sai a wannan mako rahoton ya bazama a duniya.
Kafofin watsa labarai na kasar ta Brazil sun yi ba'a dangane da wannan jarumta ta uwargidan shugaban kasar da ya sanya rahoton ya kasance kanin labarai da abin fade cikin kasar a ranar Litinin din da ta gabata.
A yayin haka kuma rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasar na Brazil, Michel Termer shine shugaban kasa mafi kasa ta fuskar shahara a tarihin shugabannin da suka shude.
Source naij.com
0 Comments:
Post a Comment