Saturday, 30 June 2018




SO NE.. PART 1

Home SO NE.. PART 1

Anonymous

Ku Tura A Social Media
karar ringtone din waya na da ya cikamin kunne da kara shine ya tasheni daga baccin da nake, nayi salati ga fiyayyen halitta, sannan na tashi daga kwance na zauna, sannan na mika hannuna a hankali na dauko waya na da nufin na daga kiran da akemin, a lokacin ne kiran ya katse, ban tsaya duba missed call din ba na ajiye wayar sannan na tashi na fita daga daki naje nayi alwala sannan na dawo na tayar da sallah. Raka'a ta biyu da fara sallah wayata ta sake daukar ringtone alamar ana kirana a wayar,wanda bayan katsewar kiran ne bata kara ring ba har na idar da sallah sannan nayi addu'o'i na shafa fatiha, a sannan ne na mike naje na dauki wayar tawa sannan na duba missed call domin naga wanene mai kirana da wannan sanyin safiya. Sabuwar lamba na gani wadda a iya tunanina ban gane lambar ba, nan fa na fara tunanin wanene wannan mai kiran da har yamin missed call guda 5, amsar da na kasa baiwa kaina kenan, sannan na fara kokarin kiran lambar, kirana ke da wuya naji ta shiga tana ring, sai da ta dan jima sannan naji an daga kiran. Shiru naji na dan lokaci ba aimin magana ba, sai na fara yin sallama, da wata sassanyar murya mai dadin sauraro naji an amsamin sallamar tare da fadin ka tashi lafiya, cikin sanyin jiki na amsa lafiya kalau sannan na tambaya wane ke kira? Sai tace Fatima ce yaya ka kashe wayar zan kiraka domin inada wata magana ne dakai, na amsa mata cikin sanyin jiki da cewa to Na kashe kiran sannan na fara wani karamin tunani a cikin zuciya ta, WACECE WANNAN ? amsar da na gagara baiwa kaina kenan ina ta sakar zuci har ta sake kirana, naji wayata na ringing.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: