Sunday, 1 July 2018




SO NE.. PART 2

Home SO NE.. PART 2

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Na danna maballin kira na wayata na daga kiran sannan na kara wayar a kunne na, sai naji ance dani 'dan allah ina magana ne da Abba?' mamaki ya kamani na amsa mata da cewa eh shine sannan taci gaba da cewa 'tun daga lokacin da na kalli hotonka naji kaunarka ta cikimin zuciyata, na kasance kullum cikin begenka, hotonka ya kasance abin kallona a koda yaushe, sai gashi kuma idan namaka message a facebook chat naka baka mini reply, hakane ya hanani sukuni na tsawon lokaci wanda har ta kai jiya da dare na kasa barci saboda tunaninka, hakan ne yasa na kasa jurewa har na kiraka a wannan lokaci domin na sanar dakai abinda ke cikin zuciyata'.
A lokacin ne naji wani abu ya soki zuciyata wanda na kasa gane menene, nayi shiru na dan lokaci, sannan nace da ita, 'naji duka uzirin ki, amma kiyi tunani cewa nifa sunanki kawai na sani, ban taba ganinki ba sannan ban san inda kike ba kuma nasan kema hakan ne, amma ya za'ai ki tunkare ni da batun soyayya?'
Fatima ta danyi murmushi sannan cikin wata sassanyar murya tace dani, 'yaya Abba ni ban damu da duk inda kake ba, nidai burina ka amince da soyayyata, wallahi idan kaki karbar soyayya ta zan fada mawuyacin hali, hotona kuma zan turo maka tare da addrees nawa'
Na sake yin shiru ina tunani sannan nace da ita 'shikenan zanyi tunani akai', haka mukai sallama da Fatima sannan na kashe kira, na ajiye wayar a gefena sannan na zauna na fara tunani a zuciyata ina jin abin kamar mafarki.
Karar message ne yasa na dawo dani daga dogon tunanin da na fada, sannan na duba wayata sai naga message guda biyu, na tsaya ina kallon wayar cikin sanyin jiki sannan na saka hannuna na bude message na farko.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: