Bani da niyyar sake tsayawa takarar Sanata ( Kwankwaso ya gayawa Buhari )
Tun bayan ganawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi da dan majalisa mai wakiltar al’ummar Kano ta tsakiya, kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwso ne dai jama’a ke ta hasashen abubuwan da jiga jigan biyu suka tattauna.
Wannan tattauna tsakanin Buhari da Kwankwaso ta wakana ne a daren Litinin, 23 ga watan Yuli a gidan shugaba Buhari dake fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja, inda shugaban APC da wasu gwamnonin jam’iyyar su hudu suka halarta.
Daily Nigerian ta ruwaito shugaba Buhari yayi nufin ganawa da Kwankwaso tare da sauran Sanatocin dake korafi tare da barazanar ficewa, amma sai gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru ya bashi shawarar ya gana da Kwankwaso a lokaci na daban shi kadai saboda muhimmancinsa.
Oshiomole ne ya fara bude taro, inda ya bayyana ma Buhari irin kokarin da yayi na lalamar Kwankwaso, tare da tabbatar da cigaba da zamansa a jam’yyar, bayan nan sai Buhari ya dauka, inda shima ya bayyana ma manufarsa na magance matsalar, tare da yi masa tayin cigaba da zama a jam’iyyar don sake taka takarar Sanata a zaben 2019.
“Zamu shiga tsakani a rikicinka da Ganduje, zamu kawo karshen wannan matsalar, don haka ba sai ka fita ba, musamman duba da irin gudunmuwar da ka bayar wajen kafa wannan jam’iyya.” Inji Buhari.
Sai dai a nasa jawabin, Kwankwaso ya bayyana kaduwarsa da yadda yake ganin kamar shugaba Buhari ya nuna bashi da masaniya game da hatsaniyar dake cikin jam’iyyar da kuma rikicinsa da Ganduje.
“Da farko dai kamar yadda na fada ma Oshiomole, bani da burin sake tsayawa takarar Sanata, bani bukatar sake komawa majalisar Dattawa, idan zaka tuna Ya Shugaban kasa, sau uku muna tattauna wannan batu, amma baka dauki wani mataki ba.” Inji Kwankwaso.
Duk kokarin da gwamonin dake wajen suka yin a tausar Kwankwaso tare da bashi hakuri, inda suka nuna masa matsayinsa a jam’iyyar da irin gudunmuwar da ya bayar, amma hakan ya ci tura, haka dai aka tashi baram baram, ba tare da wani tabbaci daga Kwankwaso ba akan ko zai zauna a jam’iyyar.
Daga cikin wadanda suka halarci wannan zama akwai gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, na Borno, Kashim Shettima, na Ogun, Ibikunle Amosun, da na jihar Jigawa, Abubakar Badaru.
Wednesday, 25 July 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Rikici ya barke tsakanin Fati Muhammed da Teema Makamashi akan soyayyar Sanata Dino Melaye.Rikici ya barke tsakanin Fati Muhammed da Teema M
Atiku yace buhari Na Tsoron Mahawara DaniDan takarar Shugabancin Kasar nan karkashin peopl
Shugabannin 'yan sanda 4 mafi girma za a iya tilasta su kamar yadda IGP Adamu ya daukaShugabannin 'yan sanda 4 mafi girma za a iya tila
ASUU Ta Janye Dogon Yajin Aikin Da Ta Shiga Tsawon Wata Uku Kungiyar Malaman Jami'o'i Nijeriya ASUU ta janye
JAMB 2019 Exam Slip Reprinting Begins 2nd MarchJAMB has disclosed that the printing of 2019 JAMB
Yan makarfi sunata kone kone na tsintsiya wacce ita tace inkiyar apc.Yan makarfi sunata kone kone na tsintsiya wacce i
0 Comments:
Post a Comment