Sabon album din da ya fita kwana biyu da suka wuce na manyan mawaka tare da matasan mawaka mai suna ” Manufarmu ” Wanda Kamfanin Abnur Entertaiment ta dauki nauyin saki duk tsakiyar shekar karkashin mawaki nura m inuwa.
Dalilin yin wannan album mawaki nura m inuwa yace”
Kamar yadda nasan ban isa na daukaka wani ba, Haka na yarda ban isa na durkusar da wanda Allah yaso ya daga ba.Ina mai farin cikin bayyana muku wannan poster a matsayin sabon Album dinmu na tsakiyar shekar wanda na yanke shawarar zan dingayinsa da mawaka a ko wace tsakiyar shekara saka makon korafin masoyana na rashin sakin Album Akai Akai da banayi , wannan shirine musamman dan bada gudunmawa ga yan uwana mawaka badan nura ya isaba ko kuma na kai kaina wani guri ba.Manufarmu itace kowa yasan da babu dan koyo da ba a sami gwani ba, salon zaici gabane har zuwa kan mawakan dama ban sansu ba indai sunda basira.A karshe ina mai jan hankalinmu da mu dogara ga Allah akan komai.
SUNAN MAWAKAN DA SUKE CIKIN WANNAN ALBUM DIN:-
1- Nura M Inuwa 2- Annur H Banur 3- Faruk M Inuwa 4- Shamsu Alale 5- Anas A Ibrahim 6- Sani B haruna 7-Ali Show
Gamai bukatar wannan Album to ya garzaya kasuwa domin siyan dai dai ko sari.
GA Waka daya daga ciki ku dandanata.
Source :- Arewablog.com
0 Comments:
Post a Comment