An kera kumbo na farko Wanda zai iya shiga cikin Duniyar Rana
Cibiyar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA, ta kaddamar da kumbonta da aka kera kan dala biliyan daya da rabi, da zai zama na farko da ya kai ga duniyar Rana.
Kumbon wanda NASA za ta harba shi zuwa zuwa sama daga jihar Florida a yau Asabar, zai gudanar da bincike ne kan wasu sirrika na tsakiyar rana, da ake kira da 'Corona', wanda masana sukai ittifakin, zafinsa ya ninka na wajen rana sau 300.
Kumbon wanda aka sanyawa suna The Parker Solar Probe zai kuma taimaka masana sararin samaniya da ke duniya, wajen hasashen lokacin da kakkarfar guguwar da ke tsananin gudu a zagayen rana ka iya ketowa doron duniyaduniya .
Kumbon dai gina shi da kaurin inchi hudu da rabi, da ke karfin bashi kariya daga karfin zafin rana mafi tsanani da ake ji a doron duniya da ya ninka sau 500, wato kwankwacin zafin digiri 1, 371 a ma’aunin Celcsius.
Ana sa ran da zarar kumbon ya kusanci Rana, gudunsa zai karu zuwa saurin tafiyar kilomita dubu 700, 000 cikin awa guda, abin da zai bashi damar zama abin da dan adam ya kera mafi sauri a tarihi.
RFIhausa.
Saturday, 11 August 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Ko An Samo Maganin Cutar HIV AIDS Kuwa,?An kasa gano cutar AIDS daga jikin wani mutum mai
An Gano Manya Manyan Dalilan Da Suka Sa Atiku Ya Fadi ZabeA halin yanzu dai za a iya cewa karshen tika-tika
A Hanlin yanxu maimaiduguri cikin damuwa anyi attacking nasu lokacin Zabe a cikin minti goma. A Hanlin yanxu maimaiduguri cikin damuwa anyi att
JAMB: 2019 UTME ƙare, 'yan takara ku shirya don fara duba sakamakon.JAMB: 2019 UTME ƙare, 'yan takara ku shirya don f
Yar gidan Sarkin Kano ta mayarwa da Ganduje raddi.Yar gidan Sarkin Kano ta mayarwa da Ganduje raddi
SOjoji sun Kashe wata yar NYSC APC a cikin Bonny, Rivers State SOjoji sun Kashe wata yar NYSC APC a
0 Comments:
Post a Comment