Rushe masallacin China ya jawo takaddama tsakanin Musulmai da gwamnati
Daruruwan musulmi a yammacin China na takaddama da hukumomi domin hana rusa masallacinsu.
Jami'ai sun ce masallacin da a ka gama gininsa kwanan nan ba shi da takardun izinin gini a Ningxia.
Sai dai musulman sun ki amincewa, inda daya daga cikin mazauna garin ya ce ba za su "yarda gwamnati ta taba masallacin ba."
China na da musulmi miliyan 23, kuma musulunci ya karbu a yankin Ningxia tsawon karni da dama da suka wuce.
Amma masu fafutikar kare hakki sun ce akwai karuwar nuna kiyayya ga Musulmi a China daga hukumomi.
An gina masallacin ne a wani salo na gabas ta tsakiya, inda ya ke da hasumiyoyi da kubbobi masu tsayi da dama.
Ya a ka fara boren?
Ranar 3 ga watan Agusta, jami'ai su ka buga wata sanarwa da ke cewa za a rushe masallacin da karfi da yaji saboda ba a bayar da izinin tsarawa da gina shi yadda ya kamata ba.
An rarraba sanarwar a shafukan intanet tsakanin 'yan kabilar Hui, kamar yadda kamfanin dillancin labarai ta Reuters ta ruwaito.
Mutane da yawa sun bukaci sanin dalilin da ya sa hukumomi ba su hana gina masallacin ba, wanda a ka gama shekaru biyu da su ka wuce, in dai har ba a bayar da takardun izinin gina shi ba, kamar yadda wata jaridar kasar Hong-Kong ta ruwaito.
Rahotanni sun nuna cewa an yi zanga-zanga a wajen masallacin ranar Alhamis kuma a ka ci gaba a ranar Juma'a. Hotunan da su ka bazu a shafukan sada zumuntan China sun nuna taron mutane mai dimbin yawa a wajen masallacin.
Har yanzu dai ba a tabbatar ba idan za a fara rushe masallacin ranar Juma'a kamar yadda a ka tsara, ko kuma idan an cimma matsaya.
Kafar watsa labaran kasar China ba ta ce komai ba har yanzu.
BBChausa.
Saturday, 11 August 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Gwamnatin ganduje ne ta fara kammala ayyukan da ta gada Gwamnatin mai girma Dakta AbdullahiUmar Ganduje O
Kalli hotunan Ɗalibin mafi kyawun rubutun hannu a duniyaKalli hotunan Ɗalibin mafi kyawun rubutun h
United State (US) Secretary of State, Calls Atiku, Congratulates Him Ahead of the PollsThe United State (U.S) Secretary of State, Secret
Yan makarfi sunata kone kone na tsintsiya wacce ita tace inkiyar apc.Yan makarfi sunata kone kone na tsintsiya wacce i
Littafin Mijin Ummmata Kashi Na Daya Zuwa Kashi Na Biyar📚 MIJIN UMMATA littafi Na DAYA 📖% Littafin yafa
Kungiyar Tijjaniyya Movement Ta Yi Kira A Zabi BuhariKungiyar Tijjaniyya SUFI Movement ta yi kira ga m
0 Comments:
Post a Comment