Monday 3 September 2018




Yan sanda sun kama shugaban makarantar firamare akan lalata yara 4 a Enugu

Home Yan sanda sun kama shugaban makarantar firamare akan lalata yara 4 a Enugu

Anonymous

Ku Tura A Social Media

Rundunar yan sandan jihar Enugu sun kama wani shugaban makarantar firamare, Idoko Nathiel mai shekaru 50 a kauyen Mkpamteulo, garin Enugu Ezike kan zargin lalata yara hudu dake karkashin kulawarsa.


Kakakin rundunar, Amaraizu, ya bayyana cewa lamarin ya faru a makarantar Migrant Farmers Children School dake garin Aguibeji na Enugu Ezike, karamar hukumar Igboeze North.

Amaraizu ya bayyana cewa jami’an hukumar bincike na musamman sun binciki mai laifin na tsawon makonni akan wannan mumunan ayyuka nasa.

Yan sanda sun kama shugaban makarantar firamare akan lalata yara 4 a Enugu
Ya bayyana cewa mai laifin a ranar 17 ga watan Yuli a wani daji kusa da makarantar ya lalata yara hudu tsakanin shekaru biyar zuwa shida.

“An tattaro cewa shugaban makarantar ya tura yatsun hannunsa a matancin yaran guda hudu, inda ya ji masu mumunan rauni har ya sai basa iya tafiya da kyau.

“An ci gaba da fadin cewa daya daga cikin daliban ne ta bayyanawa iyayenta abunda ya wakana a makarantar da shugaban ya lalata su.

Hakan yayi sanadiyan kama shugaban makarantar. Inda shi kuma ya daura laifin akan shaidan."

Ya nemi matarsa da iyayen yaran da su yafe masa, cewa wannan ne na farko day a fara faruwa.

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa a yanzu likitoci na kula da yaran yayinda aka fara gudanar da bincike.

Amarizu yace za’a gurfanar dashi a kotu da zaran an kammala bincike.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: