'YAN UWA 'YAN AREWA MASU DARAJA DA ALBARKA, WAI SHIN ME YASA MUKE DA SAURIN MANTUWA HAR MUKA MANTA DA ABINDA GWAMNATIN PDP SUKA MANA?
Marubuci: Datti Assalafy
Har mun manta a lokacin gwamnatin PDP da aka tashi rugurguza garuruwanmu gaba daya aka tilasta wasu guduwa daga gidajensu zuwa sansanin 'yan gudun hijra?
Har mun manta lokacin da 'ya'yan wasunmu da kannenmu a makarantu ana dannesu a kasa ana yankawa kamar kaji, 'yan mata budurwai a zabi na zaba a gudu dasu a mayar dasu bayi ana saduwa dasu ala tilas ana musu fyade?
Ya dace mu manta da kisan da aka yiwa manyanmu na arewa 'yan mazan jiya irinsu General Shuwa, wasu manyanmu don dole suka tsere daga Kasar suka barmu a Nigeria ana kashe mana 'yan uwa ana ruguje mana gidaje da makarantu da kasuwanni?
Ba mu bane al'ummar da aka dinga hallaka mana manya manyan malaman musulunci, a bangaren darika aka hallaka malamin Allah salihi Sheikh Adam Misrah Nafada daga jihar Gombe, a bangaren izala aka kashe mana Almarhum Malam Auwal Albaniy Zaria da wasu manyan malamai, har akayi yunkurin hallaka mana sheikh Dahiru Usman Bauchi da Sheikh Sani Yahya Jingir da wasunsu, duk mun manta?
Ba mune jama'ar arewa da aka dinga shiga gidajenmu har cikin dakunan matanmu na aure ana 'daga mana karkashin gado na raya sunnar Manzon Allah (saw) da zummar wai ana binciken kayan ta'addanci, da zaran an samu ko da gwangwanin maltina ne sai a kama mutum ace wai na hada bomb ne, yanzu har mun manta da wannan wulakanci da aka mana a gwamnatin PDP?
Ba mu bane a arewa duk wasu hazikai jarumai da suka san sirrin kwangilar ta'addancin da aka kawo don a rusamu, hazikannan suka fara tona musu asiri irinsu Malam Ja'afar Kano, Malam Albaniy Zaria da wadanda suka dinga bada shawara akan hanyoyin da za'a kawo karshen ta'addancin sai da akaci amanarsu aka kamasu aka musu sharri wasu ma aka hallakasu duk don a jaddada ayyukan ta'addanci a yankinmu na arewa, yanzu duk mun manta da wannan?
'Yan uwa musulmin arewa har mun manta da lokacin da akayi yunkurin jawo dokar hana iyayenmu mata yawo da hijabi da nikabi sai dai su fita tsirara kamar matan maguzawa arna, idan akaga musulma da hijabi sai an tilastata ta cire an taba ko'ina a jikinta an shafa wai ana laluben bomb, saboda iskanci da iye shege, yanzu duk mun manta da wannan abinda akayi mana a gwamnatin PDP?
Kai 'dan arewa musulmi da kake kalubalantar shugaba Buhari kake zaginsa, shin an ta6a yiwa mahaifiyarka ko matarka irin wannan cin mutunci da wulakanci da keta haddi? tsakani da Allah idan an taba yiwa naka haka zaka 'kara kaunar jam'iyyar PDP?
Ba mune jama'ar da aka katangewa hanyoyi saboda checkpoints tafiyar awa daya ta koma awa biyar ko shida saboda tsananin bincike da bata lokaci, idan ka dauko mahaifiyarka a mashin bata da lafiya zaka kaita asibiti dole sai ta sauka ta taka da kafa wai kar ko kuna dauke da bomb, duk inda akaga mutum da gemu kawai anga 'dan ta'adda saboda rashin mutunci da makircin arna makiya addinin Allah, garuruwanmu sun koma kamar wadanda aka cinyesu da yaki sun koma kufayi, yanzu har mun manta da irin wannan kuncin rayuwa zamu sake komawa ga jam'iyyar PDP?
'Yan uwa musulmi 'yan arewa masu albarka har mun manta da lokacin da ake ganin jirage masu saukar ungulu suna sauka a dazukan garuruwanmu suna jibge makamai kullun ace jirgi ya sauka a jeji amma ba'asan daga ina yake ba, a Maiduguri da Yobe har akayi lokacin da idan anga jirgi mai saukar ungulu ya sauka a jeji to wannan ranar sai wani bala'i ya faru, kunaji kuna gani kuma duk duniya ta gani a gwamnatin PDP aka kama jirgin shugaban kungiyar addininsu Pastor Ayo Oritsejafor shakare da muggan makaman yaki da miliyoyin daloli za'a shigo dasu Nigeria aka kama jirgin a Kasar Afirka ta Kudu, yanzu duk mun manta wannan zamu sake komawa garesu?
Tsakani da Allah a lokacin gwamnatin PDP da akace wai akwai saukin dalar amurka da arahan shinkafa, ya iya toshe mana wannan bala'in da ya afkowa arewa a lokacin?
Shin da a saka maka bomb ko a harbeka da bindigar harbo jirgin sama (AA) ya tarwatsa naman jikinka, ko ayi maka yankan rago amma a saukaka maka farashin dalar amurka da arahan shinkafa a hallakaka a kame 'ya'yanka mata ko kannenka mata a tafi dasu dazuka ana jima'i dasu, wanne yafi sauki da a barka ka rayu da tsadar dalar amurka? don wallahi yunwar ma babu ita sai dai ga rago.
Don haka 'yan arewa musumman musulmi muyiwa kawunanmu karatun ta nutsu jama'a, kar muyi saurin manta wannan cin amana da aka mana a gwamnatin PDP, kunga haka bai taba faruwa ba a jihar Abia, ko Anambra, Enugu da sauransu.
Allah Ka sa mu fahimta.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode
Source: www.MuryarHausa24.com.ng
Karanta Kaji: Manya Manyan Nasararorin da Mulkin Buhari Ya Samar a Arewacin Nigeria
Home ›
Labari da Dumi-Dumin Sa
Ra'ayi Riga
›
Karanta Kaji: Manya Manyan Nasararorin da Mulkin Buhari Ya Samar a Arewacin Nigeria
0 Comments:
Post a Comment