Tuesday, 9 October 2018




Wani matashi ya fara tattaki daga Zaria zuwa Abuja dan nuna goyon baya ga Atiku

Home Wani matashi ya fara tattaki daga Zaria zuwa Abuja dan nuna goyon baya ga Atiku

Anonymous

Ku Tura A Social Media

Wani matashi me suna, Kamaludden Bashir ya fara tattaki da kafa daga garin Zaria na jihar Kaduna zuwa Abuja dan ya nuna goyon bayanshi ga dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Matashin wanda ya fara tafiyar tashi daga Kwarbai ya bayyanawa manema labarai cewa saida ya nemi amincewar mahaifanshi suka mai addu'ar fatan Alheri sannan ya kama hanya.

Yace gaskiya farin cikin nasarar da Atiku yayi ne tasa shi wannan tafiya kuma Atikunne kadai zai iya warware matsalar da 'yan Najeriya ke fama da ita .

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu an mai fashin kudi da kuma abincin da yayi guzuri dashi amma wannan bazai hanashi ci gaba da tafiya ba, kuma yana tsammanin zai kwashe kwanaki 5 yana wannan tafiya kamin ya isa Abuja.

Ya bayyan cewa zai yi kokarin ganin ya ja ra'ayin matasa 'yan uwanshi akan hanya dan su yi wannan tafiya tare.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: