'Dole a kawo karshen rawar 'fadi ka mutu'
LABARAI DAGA 24BLOG
Wata hukumar lafiya da ke Afirka Ta Kudu ta yi kakkausar suka kan wata rawa da ake yayi yanzu ta 'fadi ka mutu", wacce mutane daga bangarori da dama ke yin ta kamar 'yan kwana-kwana da 'yan kwallo da dai sauran su.
Sunan wakar da ake yi wa wannan rawar dai Malwedhe, wacce take nufin "cuta ko rashin lafiya".
Amshin wakar shi ne "Ina fama da rashin lafiya ko kuma ina suma."
Mawakin da ya yi wannan waka dai shi ne King Monada, kuma yana fuskantar Allah-wadai daga cibiyar kula da masu fyarfyaduta ta Afirka Ta Kudu.
Hukumar Hisbah za ta kama masu yin rawar 'fadi ka mutu' a Kano
Kun san jarumin da ya yi fice wajen rawa?
Kalli hotunan shugaban Faransa a gidan rawa a Legas
Jaridar City Press ta ruwaito cibiyar na cewa "wakar tasa tana shagube ne ga masu cutar fyarfyadiya wadanda ke faduwa a duk sanda ciwon ya tashi.
"Kuma masu fama da fyarfyadiya su ne mutanen da aka fi nuna wa wariya a Afirka Ta Kudu."
Don haka kungiyar ta yi kira kan a kawo karshen wannan rawa da suka kira ta hauka.
Amma manajan mawakin Albert Makwela, ya musanta inda ya ce: "ba mu taba yin wani bidiyo da ke nuna muna abu kamar masu suma ba.
"Mutane ne kawai suka kirkiro yin hakan da kansu," kamar yadda City Press ta ruwaito.
Manajan King Monada dai ya shirya ganawa da kungiyar don tattauna matsalar.
Tuni dai wannan rawa ta fara bazuwa a kasashe irin su Najeriya, inda har hukumar Hisbah da ke jihar Kano ta yi gargadi kan yin ta.
0 Comments:
Post a Comment