Wanne dan takara Rahama Sadau za ta zaba tsakanin Atiku da Buhari?
LABARAI DAGA 24BLOG
Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood ta goyi bayan kiran da wani mutum ya yi cewa 'yan Najeriya su zabi mutum na gari a 2019 a kowacce jam'iyya yake.
Jarumar ta bayyana haka ne a cikin amsar da ta bai wa masu bibiyar shafinta na Twitter.
Tun da farko, Rahama Sadau ta wallafa wani sako wanda ke tambaya: "shin wanne dan takara ya kamata a yi wa yakin neman zabe a zabukan da ke tafe?"
Bayan da masu bibiyar shafin nata suka rika bayar da amsoshin da watakila basu gamsar da ita ba, sai jarumar ta sake wallafa sako inda ta yi tambaya: "Ina tsammani jumlar da ya kamata na rubuta ita ce 'wanne dan takara za ku zaba' maimakon 'wanne dan takara za ku yi wa yakin neman zabe.' 😉
Wanne tasiri 'yan fim za su a zaben Atiku da Buhari?
Rahama Sadau ta yi wa mai son auren ta fatan alheri
Masu bibiyarta sun bayar da amsoshi daban-daban, amma da alama amsar da ta fi burge jarumar ita ce wadda wani mai suna A.B Danbatta ya bayar.
"Kowanne mutum shi zai yanke hukunci kan shugaban kasar da zai zaba na gaba, babu wanda zai yanke maka wannan hukuncin sai kai da kanka. Amma ina bayar da shawara ga dukkan 'yan Najeriya su zabi mutum na gari ko daga wacce jam'iyya yake."
Daga nan ne Rahama Sadau ta nuna gamsuwar ta inda ta ce "Wannan ita ce amsar da nake so a ba ni 👏🏿👏🏿.Allah ya yi maka albarka 🙌🏿
Ba kamar takwarorinta na Kannywood da suka fito fili suka bayyana dan takarar da za su goya wa baya ba, da alama dai jarumar ba ta da zabi a zaben 2019.
Tuni dai jarumai irinsu Adam A. Zango da Fati Shu'uma da makamantansu suka bayyana goyon bayansu ga Shugaba Muhammadu Buhari.
Sai dai jarumai irinsu Sani Danja da Fati Mohammed da Maryam Booth sauransu sun ce tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar za su zaba a 2019.
Masu sharhi na ganin jaruman Kannywood ka iya sauya akalar zaben 2019, wanda aka kaddamar da yakin neman zabensa ranar Lahadin da ta wuce.
0 Comments:
Post a Comment