Sunday, 11 November 2018




FATIMA ZAHRA PART 01

Home FATIMA ZAHRA PART 01

Anonymous

Ku Tura A Social Media

Fatima Zahra yarinyaya ce da
bata wuce shekara bakwai zuwa
takwas ba tana ta faman ihun a sai
ruwa mai sanyi pure water ruwa mai
sanyi daka taga mota ta tsaya saita
ruga da gudu tana ihun ruwa mai
sanyi haka tai tayi yayin da duk
sauran masu saida abubuwan maza
ne koda zaka ga mace Zaka ganta
babba wacce zata kai sha daya
shabiyu, sai da yamma tayi likis
sannan ta fara azaman tafiya gida
domin yanayin garin kaman za"ayi
ruwa, sauri sauri gudu gudu takeyi
tana Allah Allah taje gida dan tasan
Yau mai kwatanta sai Allah, gashi
tayi yamma ga ruwan da ta dawo
dashi jibge kwata2 Wanda aka siya
baifi guda shida ba, tana isa Kofan
gida gabanta ya fara dukan uku2 da
lanbo ta shiga gidan ji tayi ance
uban wa kike boyewa shegiya ko
za'ayi halin gadon ne na sata ake
lambo, dafatan badai kudina aka
zubar ba duk masifan da inna Larai
takeyi bata lura da sauran ruwan da
fatima ke dauke dashi ba saida ta
dauko fitila ta haskota sannan tace
kan uba yanxu haka kika dawo da
ruwan baki saida ba? mai bakin hali
wato kema kin dauko halin uwarki
ko to wlh Yau sai naci uwarki inga
Wanda zai kwace ki mai daure miki
gindi baya nan naga mai kwatanki,
nidai duk wannan fadan da inna
Larai keyi hawaye kawai nake ina
kallonta domin nasan Yau mai
kwatata sai Allah, babban abunda ke
damuna shine yanda take zagin
mahaifiyata gashi bata raye duk da
karancin shekaruna abun yanamin
ciwo, ji tayi an fisgota ana tsula
mata wata igiya Wanda bazata iya
gane wace iri bace, amma tsananin
zafin da takeji zata iya cewa da
icene sai tsula ihu takeyi tana dan
Allah kiyi hakuri wlh gobe duka zan
siyar amma ita ina bata ma San
tanayi ba saida ta mata likis sannan
tace Ya'u wlh baki da kwano a
gidan nan mai kama da mayu haka
inna ta shige ta barni a nan a
kwance inata kuka jikina namin
azaba ga wata shegiyan yunwa
dake kwakulanta haka ta gaji da
kukan dan kanta ta tashi ta shige
soron gidan ta kwanta domin nanne
wajen baccinta in Malam baya
gari,aiko ko kaman jira ake ta tashi
aka tsuge da ruwa, Wanda aketa
tsawa mai karfi duk ta tsorata da
tsawan da akeyi ga yunwa tana ji
kaman daka sama taji muryan inna
Larai tana fadin mayya gashi ki
ci,wani gutsirararran tuwo ne
Wanda bazai wuce loma Biyar ba
haka ta dauka da Sauri ta fara ci
inna ta wuce daki abunta ta barta
anan sai alokacin fatima Zarah ta
danji dama dama sannan ta kwanta
ga sanyi tanaji haka bacci barawo
ya dauketa, ji tayi anna kwara mata
ruwa akai da Sauri ta mike firgit
tana fadin inna Larai ina kwana, ta
galla mata harara da ban kwana ba
zaki ganni munafuka sai iya zance
kaman wata karuwa maza kije ki
dibo min ruwa mayya kawai jiki na
bari na wuce na dauki guga na fara
jidan ruwa bayan na gama cika
komai na dauko wanke wanke nayi
naje na sameta a daki nace mata na
gama tace tunda asaran ruwa
kikemin kullum sai kin dawo da
saura ingo kudin nan kije ki auno
min gyada kuma kika dade saina
kusan kasheki tayi sauri tace mata
to ,ta fita tanata Sauri dan kar ta
dade duk yan unguwar su sun San
halinda take ciki suna tausaya mata
amma ba Wanda ya Isa ya sami
inna Larai ya mata magana domin
masifaffiya ce kowa tsoranta yake.
Duk da so da yawa wasu daka yan
unguwan sukan tari malam Usman
su fadamai halinda 'yar tashi ke
ciki, amma koda sun fada baya
iyama inna larai magana, Malam
Usman irin mutanen nan ne masu
kauda ido akan abu, komai zaiyi
baya yanke hukunci akan abu sai
dai inya gani da idonshi, duk da
yawan fada mai da akeyi baya yarda
domin yanda yake ganin inna larai
naji da fatima zarah, kamar ita ta
haifeta, fatima ta gama dafa gyadan
inna Larai ta dauko gwan gwanaye
ta fara zubawa a ciki tanayi tana ci,
tana galla ma fatima harara, harta
gama zuba gyadan ta dago da kai
ta kalli fatima, wlh Yau idan kika
sake kika dawo da sauran gyada
gidan nan wlh saina kusa kasheki
domin dagan gan kike sani asara
mai bakin hali kawai, kaina na kasa
ina sauraranta. Sai jin rankwashi
nayi a kaina kinaji na kin ki kitashi
ki dauka, wato ga mahaukaciya na
magana ko, fatima tai sauri ta mike
sannan tai kasa dakai tace inna
larai yunwa nakeji kaman zan...
Bata karasa ba taji saukan mari
wanda gaba daya ta dauke wuta dan
azaba, nan da nan tasa hannu kan
fuskan tana shafa wajan yayin da
wasu zafafan hawaye ke zubo mata
akan fuska, ga yunwa ga duka, inna
larai ta fara bala'i, wato ke har kinyi
bakin da zaki kalli tsaban idona kice
min wani yunwa kike ji? dan kin
raina ni, to bari kiji Yau kwata2 baki
da kwano a gidan nan, inko kinga
kinci abinci a gidan nan to kin saida
min gyadan nan, shegiya mai suffan
mayu, bazaki dauka ki fitaba saina
kara miki? Cikin sauri ta dauka, inna
larai ta bita da harara tana ta ban
bamin bala'i wlh gyada ta ta dari
uku da ishirince inko aka batar min
da kudi Yau sai na kasheki har
lahira, karuwa kawai, fita tayi tana
tafiya tana kuka, a kullum tana
tunanin mai kalman karuwa ke nufi
da mayya, wannan kalman da inna
larai kemin suna tsayamin a rai
inaso in san miyesu dan nasan ba
abu mai kyau bane kalman, ji tayi
anata kwada mata kira daga baya ko
ba'a fada ba tasan amina ce kawar
ta, da gudu ta iso gareta tana fadin
tun dazu nake ta kiranki baki jiba,
ta ce kiyi hakuri banji bane, tace to
shikenan dama inna ce ta aikeni
siyo gyada saina hango ki saida na
matso na ganeki, tai sauri ta sauke
na nawa zaki siya tana tambayan
tana murmushi dan zatayi ciniki
tace na hamsin, baki inna tayi shine
za'a basu nan da nan fatima ta
bata. Sannan amina tace kwana
biyu baki zo makaranta ba malam
zai miki dukan fashi gashi anyi kari,
nan da nan fatima ta zaro ido waje
tace amina kin San sai baba nanan
inna larai ke barina in tawo
makaranta in kuma ya koma bata
barina ta karashe maganan da kuka,
amina tace ki tafi tallanki karki
makara zance ma Malam baki da
lfya, fatima Zarah tayi murmushi,
tana fadin ngd, bari in tafi. Kai
tsaye bakin titi ta nufa, duk motan
data tsaya zataje tana musu tallan
gyada yayinda mutane keta siya,
bata wani dade ba aka siye
duka,tana ta murna ta siyar domin
yunwa takeji, tasan inna larai zata
bata tunda ta siyar kai tsaye gida ta
nufa da sauri, gidan shiru alaman
inna larai na daki,ta shiga dakin da
sallama,inna larai dake kwance tai
sauri ta mike tana mata wani kallo,
nan da nan fatima ta dauko kudin ta
bata, ta amsa ta kirga taga dai dai
kudinta, tace yau kin fita, ta dauko
wani tuwo a kwano alaman ita taci
ta rage ta mika mata tace gashi
mayya kin min wani wiki wiki da ido
wlh kurwana kur yafi karfinki, nidai
waje nayi domin yunwa nakeji, haka
na zauna na gama cin towun
sannan na dauko wanke2 nayi, naje
na sami waje na zauna saigata ta
fito tana mata wani kallo, wato dan
bakin ciki bazaki zo ki amsa kudin
gyadan ki siyo ba shine kika zo kika
zauna wato ni zan fita in siyo, ta
mike da sauri tana fadin kiyi hakuri
inna bakice min za'a siyo ba ne, ta
gallah mata harara tare da fadin
dallah yimin shiru munafuka, ta
jefomin kudin na dauka na fita zuwa
kasuwan naje na siyo, ina shiga
gida sai jin duka nayi an rufeni
dashi wajan uban wa kike zuwa
idan na aikeki kike dadewa? Tana
kuka tana fadin wlh banje ko ina ba
saida ta mata lilis sannan ta kyaleta
dan kanta, kaman ta sama wata
babba haka ta tashi dakyar ta nufi
Haka fatima zarah taita zama cikin
sauro har yamma tayi gashi tana so
taje tayi sallah tana tsoran shiga
saboda inna Larai dan sau da yawa
inta dauko buta zatayi alwala saita
hanata tace bazata yi sallah, ba
kina mayya kice zakiyi sallah, sai
dai ta dinga yi a boye, haka ta tashi
ta lallaba ta dauko buta ta dawo
sauron tayi alwala ta fara sallah
harta idar inna bata fito ba, saida
gari ya fara duhu anata kiran sallan
magrib kafin inna ta fito ta nufo
sauro din alokacin ina zaune na kife
kaina da gwiwana hawaye na zuba
a idona, sau da yawa inajin mutane
nacewa uwa dadi gareta amma ni
ban San dadin uwa ba na taso cikin
kadaici da wahala tun ban kai haka
ba, sau da yawa nakan so dama
nima mutuwa nayi da wannan
wahalan rayuwan, ji tayi an ran
gwasheta a kai tai saurin dago wa
ganin inna larai tayi tana huci, wato
kina jina ina kiranki kikai banza
dani dan ki nunamin wato ke kin
riqa ko, kamata tayi ta rufeta da
duka tana ta kuka domin indai
wannan ne ta saba shanshi wajan
inna larai, arana saita bigeta sau
uku sau biyu, saida ta gaji dan
kanta ta kyaleta sannan tace maza
kizo kimin wanki domin kayana sun
taru, ta tashi jiki na bari ga ciwon
da jikinta yake mata haka ta mike ta
dauko wankin da uban yawa gashi
dare yayi har an gama Kiran magrib,
inna Larai tace wlh idan kika min
Jika Jika saina ci uwarki mayya
kawai, fatima dai shiru tayi ta fara
wankin ga jikinta duk yayi tsami na
dukan data sha ga hannunta na
zafi, haka dai tayi ta wankin bata
gamaba sai wajan 10 na dare, ta
nufi dakin inna larai ta shiga da
sallama amma bata amsa ba tace
inna nagama ko kallonta batayi ba
ta mike ta nufo waje tana haska
kayan, da fitila, ji kake tas ta wanke
mata fuska da mari yanzu wannan
kayan ne ya fita saboda iskanci kin
min asaran sabulu kega muguwa ko
ta kara wanketa da mari Wanda
saida ta tsugunna dan azaba ta rike
wajan tana kuka Wanda hawaye ne

Zamu Cigaba...

Share this


Author: verified_user

0 Comments: