Fitacciyar jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi addu’a ga wani “masoyinta” wanda ya roki Allah ya ba shi matar kamarta.
Shi dai Khamisu S. Guyaba ya wallafa sako ne a shafin Twitter inda ya nuna matukar son da yake yi wa Rahama domin ya aure ta.
Sai dai ya kara da cewa idan hakan ba za ta yuwu ba yana so ya auri mai hali da ilimi da nutsuwa da kuma taimakon jama’a kamarta.
Masu bibiyarsa a shafin Twitter sun taya shi addu’a inda wasu ke cewa Allah ya cika masa burinsa yayin da wasu ke yi masa addu’ar zabi mafi alheri.
Daga bisani ne jarumar ta ba shi amsa inda ta roki Allah ya ba shi matar da ta fi ta sannan ta yi masa godiya. Amsar Da Rahama Sadau Ta Bawa Wani Da Yacce Zai Aure Ta
“Allah ya ba ka wacce ta fi Rahama da komai. Na gode sosai,” in ji jarumar.
0 Comments:
Post a Comment