Tuesday, 13 November 2018




FATIMA ZAHRA PART 3

Home FATIMA ZAHRA PART 3

Anonymous

Ku Tura A Social Media

banbanci, suma sai an basu, Malam
tanimu yace Hajara Yaron nan duk
abunda na bashi bai kamata kiyi
bakin ciki ba domin shine Wanda
yake taimaka min, ni bani da karfin
da xanyi wannan aikin na gona, duk
shi keyi sannan yaje ya saida,don
na bashi wannan kyautan miye abun
bacin rai, a haka dai aka daura
auren usman da Hafsat,Wanda
Amarya ta tare a gidanta, Hafsat
macece mai hakuri gashi bata San
hayaniya, tun farkon xuwanta gidan
ta fahimci haka, domin in taje gaida
inna Hajara bata ansawa sai dai
tasha bakaken maganganu, ita inna
karima kunyan Hafsat take saboda
matar danta ce tafari kuma dan
auta, Haka Inna Hajara taita wahalar
da Hafsat in Malam tanimu baya
nan, ita kuma inna karima bata
magana,ta bata wanki wanke
wanke,girki, shi Usman yana fama
da gona sai yamma yake
dawowa,bai San maike faruwa ba,
kuma Hafsat bata taba fada mishi
komai ba, a haka dai ake ta zama a
gidan, wata Yar Kanwan inna Hajara
ce tazo daka, Zaria mai suna larai
auranta ya mutu tazo domin, inna
Hajara ta kaita wajan boka don
samun wani mijin aiko tana ganin
usman tace ga miji ta samu, larai
macece masifaffiya bata da hakuri
gabin malamai,auranta uku, tunda ta
fito a na ukun ta rasa manemi shine
tazo wajan innanta Hajara don ta
nema mata mafita, to gashi taga
Usman ta mutu a kanshi, inna
Hajara taji dadi sosai saboda indai
larai ta aureshi in Malam tanimu ya
rasu tunda Usman dinne namiji ai
komai nasu ne, alokacin,Hafsat na
dauke da cikinta na wata biyu, larai
ta tsana Hafsat ko ganinta bata
kaunar yi, gashi Usman ko kallo
larai bata isheshi ba, a haka suka
shirya suka nufi wani daji mai uban
nisa, sukai ta hawa tsaunika, suna
zuwa kan wani dutse sukaji wani
karan ihu tare da hayaki, sai ganin
mutum sukayi a gabansu, sai faman
tashin wari yake,ya bude baki yana
wani irin dariya, hakoranshi duk
datti har green2 yayi saboda datti,
lokaci daya kuma ya dake,a nan
inna Hajara ta fara mai kirari, boka
namu, biyan bukata na wajanka, azo
ka biya bukata, a butulce maka aga
tashin hankali,ya kwashe da dariya
sannan ya gimtse fuska,ya daga
hannu saiga wani qoqo a
hannunshi da wani farin ruwa
kaman nono a ciki,saiga Usman da
Hafsat da inna karima a ciki,La
[truncated * Tare da ware ido ta dan
rike inna Hajara,boka ya kwashe da
dariya, lokaci daya kuma ya gimtse
fuska kaman bai taba dariya ba,
yace zamu biya miki bukata, zaki
aureshi kaman yanda kike so,amma
dole sai an kashe mahaifiyarsa,
shine auran zaiyi, don tana yawan
tsayuwan dare tana mai addu'a,
itama sai tana al'ada zamu yi aiki a
kanta, tunda ya fara bayani ido larai
ta zuba mai harya gama, sannan
yace mai kukace,inna Hajara tai
saurin cewa mun yarda, a aikata
komai indai zata aureshi, boka ya
kwashe da wata shegiyar dariya, da
wani ihu mai uban karfi Wanda ni
kaina saida waya ta ta fadi daga
hannu na dan tsoro ita kanta larai
ta tsorata, amma inna Hajara ko
dar, batai ba, wani irin hallita ne ya
sauka a gaban su mai ban tsoro,
komaif na halittan rabi ne, yana rike
da wata kwalba yaba, ya amsa
sannan ya bace, boka ya mika ma
larai yace wannan turare ne, ki
dinga zubawa a ciki inya kare,
komai kika cemai shi zaiyi, sannan
ya mika mata wani qoqo yace ta
shanye abunda, ke ciki ta amsa
takai baki duk tsami abun ga wari
haka ta amsa ta shanye, ta mika ma
bokan sannan suka ajiye mai kudi,
ya bace, suma suka bar wajan da
sauri, kai tsaye gida suka nufa,tun
daka ranan larai ta fara amfani da
turaren, Usman ya dawo daka gona
yana ganinta duk ya gigice, ya rude,
wani azaban sonta yaji yana yi, ya
sakar mata murmushi itama ta
maida masa martani, a ranan kuma
inna Hajara ta fara ciwon ciki da
zazzabi tare Ciwon kai,tundaka
ranan ciwo sai kamari yake, yayin
da Usman ke kara son larai a ransa,
har Hafsat ta gane, amma bata mai
magana ba don tana da zurfin ciki,
inna Hajara ko magana bata iyayi
balle kuma cin abinci, duk Malam
tanimu ya shiga damuwa sosai,
akan ciwon, u juma'a garin anyi
sanyi sosai a ranan inna Hajara ta
cika ta koma hannun mahaliccin ta,
anyi ma Malam tanimu, mutuwan
data girgiza shi,alokacin da aka
Sanar masa, a lokacin saida ya
sume domin karima macece ta gari
yana sonta, haka rayuwa take,
Usman ko kukan ma ya kasa yi sai
kallon mutane kawai yake, Hafsat
itama tayi kuka na rashin sirikanta
mai sonta, haka aka shirya ta aka
kaita makwancinta na gskiya a g
dawowa daka makabarta shima
Malam tanimu ya fadi, jama'a akayo
kansa da sauri, ana dubashi, shima
dai rai yai halinsa, a gskiya anyi
musu mutuwan data girgiza Su
tabbas inna Hajara taji mutuwan
mijinta, Usman ko shima saida ya
sume, suwaiba da jamila suma
sunzo anyi zaman makoki, saida
akayi bakwai kafin kowacce ta
koma dakin mijinta, a nanne larai ta
matsama Usman akan batun
auransu aiko ba musu ya yarda,
akasa biki sati daya, aiko mutane
suna ta magana daka yin bakwai sai
aure sai kace Wanda bai damu da
mutuwan ba,aikin asiri kenan Allah
ya tsare mu tare da zuri'ar musulmi
baki daya daka fadawa shirka,aiko
Hafsat ba karamin tashin hankali ta
shiga ba don ko abinci sau daya
ake bata duk ta rame, Usman shima
ya daina kulata daka yaje wajanta
sai yaga kaman ana Sara mai wuka
a kai, haka akayi auran, Amarya ta
tare a dakin mahaifiyarshi,aka sata,
aiko a nan suka rakashe akaci
amarci, tun daka ranan ya daina
tunanin Hafsat yama manta da
ita,Inna hajara da Larai suyi ta gana
mata azaba,itace musu wanki,
shara, wanke 2 duk wani aiki na
gidan ita keyi tayi girki su hanata
sai sunga dama, a kwana a tashi ba
wuya har cikin Hafsat yakai watan
haiyuwa, da yan uwanta sukazo
inna hajara tace Su koma zata kula
da ita,haka suka koma suka barta,
badan son ransu ba don yanayin da
suka ganta gskiya ba karamin
tsorata sukayi ba Hafsat kyakyawa
ce ta karshe, amma duk ta rame
tayi wani baki sai kanta yayi girma
kaman mai cuta, to sai suka dauka
ko cikinne yasata haka,gashi ita
batace musu komai ba,wani zubin
har dukanta suke ga tsohon ciki,
Ya'u tunda Hafsat ta tashi tayi
wanke2 ta take jin maranta na ciwo
ko shara bata samu tayi ba tashiga
daki, aiko inna Hajara na fitowa
taga datti, ta shiga dakinta da nufin
yi mata bala'i saita tsaya turus
domin ganin tana na quda, aiko da
sauri ta fito, ta kwadawa larai kira
ta fito, aiko itama ta shigo tana
wani tabe baki kaman taga kashi,
suka kwashe da dariya, itako hafsat
tana ta faman nishi tana Ku taimaka
min amma sunyi mata banza, inna
Hajara harda tun kudeta,larai kuma
ta danna mata ciki da karfi aiko nan
ta saki wani ihu mai karfi nan take
ko tai wani nishi mai karfi saiga
baby ta fito tana tsala kuka, jin
Hafsat din shiru yasa larai ta
zungureta a kafa amma bata motsi
aiko suka, taba ta anan ne suka
gane ta rasu, itama Hafsat Allah ya
mata cikawa, koda lbri ya iske
Usman saiya tsinci kanshi dayin
kuka sosai, har aka kaita gidanta na
gskiya, makwabtansu ne suka ma
yarinyan data Haifa wanka yarinyan
kyakyawa duk Wanda ya ganta sai
yace tubarkallah masha Allah tare
da tausaya ma yarinyan, Usman
yana ganin yarinyan yaji wani sonta
ya shigeshi aiko ya rungumeta yana
kuka, Wanda larai da inna Hajara
abun ya basu mamaki sun ce ko
dole Su koma wajan boka, aiko
anan ya mata huduba da fatima
zarah, sunan diyar manzon Allah,
kuma sunan mahaifiyar Hafsat, aiko
yan uwan Hafsat din sunji dadi
saida akai bakwai sukai haraman
tafiya suka ce Malam Usman ya
basu Yar yace suyi hakuri yana
bukatar ta kusa Dashi domin ita
zata dibe mai kewan rashin da
yayi,haka suka tafi badon sunso
haka ba, a washe garin ranan suka

Share this


Author: verified_user

0 Comments: