Kotu ta haramtawa NLC da TUC shiga yajin aiki
LABARAI DAGA 24BLOG
- Kotun Mai'akata na kasa ta bayar da umurnin cewa kungiyar kwadago na kasa ta janye yajin aikin da take niyyar farawa
- Kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan gwamnatin tarayya ta shigar da kara kotun inda tace yajin aikin zai kawo cikas ga tattalin arzikin kasa da lafiyar al'ummma
Kotun Ma'aikata na Najeriya ya haramtawa Kungiyar Kwadago na kasa (NLC) da Kungiyar Masu Sana'o'i na Kasa (TUC) shiga yakin aikin da suka sanar da cewar za su fara a ranar 6 ga watan Nuwamba.
Justice Sanusi Kado ne ya bayar da bayar da wannan umurnin a yau Juma'a sakamakon karar da gwamnatin tarayya da shigar da hannun lauyanta na Ma'aikatar Shari'ar na kasa, Mr. Dayo Apata.
Yanzu-yanzu: Kotu ta haramtawa NLC da TUC shiga yajin aiki
Kotun ta amince da dalilan da Apata ya bayar inda ya bayyana cewa idan aka shiga yakin aikin, tattalin arzikin Najeriya zai raunana kana 'yan dimbin Najeriya za su rasa damar zuwa asibitoci domin kula da lafiyarsu.
Kungiyar Kwadagon tayi barazanar fara yakin aikin ne a ranar 6 ga watan Nuwamba domin tilastawa gwamnati kara adadin albashi mafi karanci wadda a yanzu ya ke N18,000.
A tattaunawar karashe da gwamnati tayi da kungiyar kwadago, Gwamnatin tarayya ta ce za ta iya biyan N25,000 yayin da Kungiyar gwamnonin Najeriya suka ce su N22,500 za su iya biya.
Justice Kado ya daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Nuwamban wannan shekarar.
0 Comments:
Post a Comment