Shugaba Buhari yace kowa ya zabi wanda yake so
LABARAI DAGA 24BLOG
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yanzu kam 'yan Najeriya tuni suka waye domin kuwa lokacin murdiyar zabe, satar akwati da kuma anfani da hukumomin gwamnati don yin magudin zabe dukkan su sun wuce.
Haka zalika shugaban kasar ya kara da cewa yana shawartar 'yan Najeriya a ko'ina suke da su darje su zabi wanda ran su ke so a zabukan gama gari na shekarar 2019 masu zuwa a dukkan matakai.
Ba sauran sak: Shugaba Buhari yace kowa ya zabi wanda yake so
Shugaban kasar yayi wadannan kalaman ne lokacin da ya karbi bakincin wasu manyan jami'an majalisar dinkin duniya da kuma shugabannin kungiyar kasashen yammacin Afrika a ofishin sa dake Abuja.
Haka zalika shugaban kasar ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatin sa zata yi dukkan iya kokarin ta wajen ganin zabukan na 2019 sun kasance sahihai a kowane irin ma'auni.
Friday, 2 November 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Buhari sun tattauna da tsohon shugaban majalisar wakilai na kasa.Buhari sun tattauna da tsohon shugaban majalisar
Buhari ya samu kashi 9 daga cikin 23 a cikin Sakkwato, Atiku 3.Buhari ya samu kashi 9 daga cikin 23 a cikin Sakk
Atiku ya rushe Buhari a yakin Kwankwaso . Atiku ya rushe Buhari a yakin Kwankwaso .Shafin F
INEC ta bayyana jihar da mafi girma yawan adadin PVCs (Full List) Shugaban Hukumar INEC Mahmood YakubuINEC ta bayyana jihar da mafi girma yawan adadin
Wasu 'yan APC hudu da aka kama tare da takardun jefa kuri'a, bindigogi a Legas NATIONAL NEWS. Wasu 'yan APC hudu da aka kama tare da takardun j
Buhari 44 - 0 Atiku - APC ta lashe dukkan karamar hukuma 44 a Kano. Buhari 44 - 0 Atiku - APC ta lashe dukkan karamar
0 Comments:
Post a Comment