Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta bayyana cewa a kaf cikin malaman zamanin nan babu wanda taji zuciyarta take so a matsayin mijin aure kamar shahararren malamin addinin Islama na kasar Zimbabuwe, Ismail Ibn Musa Menk wanda aka fi sani da Mufi Menk.
Ummi da ta saka hoton Menk a dandalinta na sada zumunta da muhawara ta ci gaba da cewa, amma dan Allah a gafarceta idan abinda ta fada akwai kuskure a ciki, ni macece wadda bana boye abinda ke zuciyata shi yasa na fito na fada kuma ba dan komai nake sonsa ba sai don Allah.
0 Comments:
Post a Comment