A farkon wannan makon ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da taken kamfen din sa na yakin neman zaben 2019 wato ‘Next Level’ wato kenan shirin daukar kasar zuwa mataki na gaba.
Shugaban kasar ya bugi kirjin cewa ya gina kakkarfan ginshikin zaunar da Nijeriya a kan turbar ci gaba.
An dai fara kamfen tun a ranar Lahadi da ta gabata, inda aka bude ake fafutukar neman kujerar shugabancin 2019 tsakanin Buhari da ke kan mulki a karkashin APC da kuma Atiku Abubakar a karkashin jam’iyyar PDP da dai sauran jam’iyyun siayasar kasar.
Buhari dai ya sha alwashin cewa idan aka sake zaben sa, to zai kara cicciba Najeriya zuwa mataki na gaba, watau matakin dauwamar da kakkarfa ingantaccen tattalin arzikin kasa.
Ga wasu manyan alkawara biyar da shugaban kasar ya dauka kamar haka:
1. Samar da ayyukan yi ga al’umman kasar
Shugaban Kasa Buhari ya yi alkawarin samar da aiki ga matasa miliyan 10 a karkashin N-Power da kuma samar da aiki a fannin sana’o’in hannu ga matasa milyan 10.
Sannan kuma ya sha alwashin samar wa milyoyi aikin yi ta hanyar bada lamuni ga manoma miliyan daya, inganta Tsarin Kiwon Dabbobi wanda zai samar da aiki ga mutane milyan 1.5. samar da kindirmo, fata, nama, amfanin gona, inganta aikin noma da kuma samar da taraktoci da za su samar wa matasa milyan 5 aikin yi.
Hakazalika ya yi alkawarin samar da dala milyan 500 domin kananan masana’antu su samar da aikin yi ga mutane dubu 500. Sannan kuma za a yi wa matasa 20,000 horon sana’o’i.
Ya kuma yi alkawarin samar da aiki ta hanyar kirkiro Masana’antu Shiyyoyi da Shiyyoyin Inganta Tallain Arziki na Musamman da sauran su.
Daga karshe Buhari ya yi alkawarin kara samar da aikin yi 300,000 ga masu talla da manoma ta hanyar kara yawan daliban da za rika ciyarwa a makarantu daga milyan 9.2 zuwa milyan 15.
2. Tallafi ga masu kananan sana’o’i
Buhari ya yi alkawarin bayar da tallafi ga masu kananan sana’o’i da karamin jari irinsu ‘trader moni’ da sauran hanyoyin samar da sana’o’i a saukake.
Ya ce idan aka sake zabar shi wasu matasa milyan 10 za su samu aikin yi a karkashin wannan tsari, fiye da milyan 2.3 da ya ce sun samu a wannan zangon na sa da ake ciki.
3. Samar da ababen more rayuwa
A nan Buhari ya sake daukar alkawarin gina hanyoyin na jiragenn kasa, Babbaar Gadar Kogin Neja ta 2, samar da hasken lantarki ga jami’o’i da kasuwanni 300 ta hanyar hasken sola, da inganta hasken lantarki zuwa migawat 12,000 da sauran su.
4. Bangaren kiwon lafiya da inganta ilimi
Buhari yayi alkawarin gyara makarantu 10,000 a kowace shekara, sannan a bangaren lafiya kuma ya ce za’a sama wa masu karamin karfi inshorar kiwon lafiya ta yadda za a rika rage musu kashi 40 cikin na dawainiyar magunguna.
5. Jawo jama’a a gwamnati
Buhari ya yi alkawarin bai wa mata kaso 35 bisa 100 na mukaman da aai raba idan ya sake yin nasara a zaben shugaban kasa a 2019. Zai kara samar wa matasa aiki a cikin gwamnati kuma matasa sabbin kammala jami’a za su rika samun aiki a karkashin ministoci da manyan ma’aikatan gwamnnati na hukumomi.an tsaron da suka kafa a kauyen.
0 Comments:
Post a Comment