Ni ne na kafa APC, ba kuma zan fita daga cikinta ba - Gwamnan jam'iyyar
LABARAI DAGA 24BLOG
Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya karyata jita-jitar da wasu ke yadawa na cewa zai fice daga jam'iyyar APC sakamakon rikicin zaben cikin gida na gwamna da ke faruwa a jihar.
A hirar da ya yi da manema labarai a gidan gwamnati bayan ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari a yau Alhamis, Okorocha ya bayyana cewa ziyarci shugaban kasa ne domin tattauna wasu abubuwa da Adams Oshiomhole ke yi a wasu jihohi.
"Ba zai yiwa in gina gida ba sannan daga baya in bar ma wasu su kwace gidan, Ina nan daram a APC, ni ne na kirkiri sunan APC saboda haka jam'iyyar mu ne kuma zamu cigaba da aiki domin cigaban jam'iyyar," inji Okorocha.
Ni ne na kafa, ba kuma zan fita daga cikinta ba - Gwamnan jam'iyyar
Okorocha ya ce abubuwan da Oshiomhole ke aikatawa na raba kawunnan 'ya'yan jam'iyyar inda ya kara da cewa babu hannun shugaba Buhari cikin tabargarzar da Oshiomhole ke aikatawa.
"Oshiomhole yana gaban kansa ne kawai, fadar shugaban kasa ba ta bashi goyon baya cewar ya kwace tikitin zabe daga hannun wadanda su kayi nasara ya mika wa wadanda suka fadi zabe ba.
"Ina kira da Oshiomhole ya rika biyaya ga doka da kuma biyaya da umurnin kotu a wuraren da suka dace, ba dai-dai bane jam'iyya ta rika watsi da umurnin kotu.
"Ya zama dole mu dauki mataki domin kiyaye mutunci da kimar jam'iyyar mu saboda zuwarsa ya kamata ya kawo farin ciki ne amma akasin hakan ke faruwa yanzu," inji Okorocha.
Friday, 2 November 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Shugaba Buhari ya yi alkawarin ba da izini na matasan matasa idan an sake zabeShugaba Buhari ya yi alkawarin ba da izini na mat
SARAKI YAYI RANTSUWA A ALFA AS NEW KOGI-EAST SENATOR. SARAKI YAYI RANTSUWA A ALFA AS NEW KOGI-EAST SENA
Abinda Atiku ya ce bayan da Hukumar INEC ta dage zaben 2019Abinda Atiku ya ce bayan da Hukumar INEC ta dage
'yan sanda sun kama maza tare da takardun kuri'u 14 a Kano 'yan sanda sun kama maza tare da takardun k
Bugu da kari: Buhari a halin yanzu yana jagorancin INEC yana da nasaba da sakamakon zabenBugu da kari: Buhari a halin yanzu yana jagoranci
Duba Kalmomi 7 masu karfi da Atiku ya furta a lokacin da akayi taron PDP NEC a yauDuba Kalmomi 7 masu karfi da Atiku ya furta a lok
0 Comments:
Post a Comment