Rundinar sojin Nijeriya ta fara shirye-shiryen gabatar da jana'izar Marigayi Manjo Janar Idris Alkali, an fara gudanar da hidimar jana'izar ne a yau tare da cikakken karramawa gare shi.
Jama'a daga ganin shirin da sojoji suke yi kunsan hakika an taba sojoji, kuma dokar aikinsu zatayai aiki akan wadanda suke da alhakkin salwantar da rayuwar Janar Idris Alkali, kamar yadda Birgediya Janar Umar Muhammad yace burinsu guda uku akan bacewar Janar Idris ya kammala.
-Na farko burin a samo motarshi kuma an samo
-Na biyu shine a tabbatar yana raye ko ya mutu, kuma an tabbatar ya mutu
-Na uku a samo gawarsa kuma an samo, dukkan hujja da dalili da suke nema ya kammala saura hukunci ya biyo baya bisa dokar aikin soji da na Kasa
Daga karshe muna jinjina ga dakarun sojoji da na 'yan sanda wadanda sukayi aikin binciken gano makomar Janar Idris Alkali karkashin jagorancjn Birgediya Janar Umar Muhammad, tabbas sunyi kokari, sun nuna bajinta da kwarewa, miliyoyin 'yan Nigeria sunji dadin hakan. Allah Ya saka muku da alheri.
Yaa Allah Ka jikan Janar Idris Alkali
Yaa Allah duk wanda yake da hannu a cikin kisan da aka masa Ka sa yayi mutuwar wulakanci fiye da yadda suka wulakanta gawar Janar Idris Alkali.
0 Comments:
Post a Comment