Shugaban kasa Buhari ya zauna da wasu Gwamnonin APC a fadar sa
LABARAI DAGA 24BLOG
- Wasu Gwamnonin Kasar Yarbawa sun gana da Shugaba Muhamamdu Buhari jiya a Villa
- Daga cikin wadanda su kayi wannan zama na bayan labule akwai Gwamnan Jihar Ondo
- Ana kokarin shawo kan matsalar da ta ke cikin Jam’iyyar APC ne kafin babban zaben 2019
Wasu Gwamnonin kudu sun gana da Shugaban kasa
Mun samu labari daga manema labarai a jiya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da wasu Gwamnonin Jam’iyyar sa ta APC mai mulki a Ranar Lahadin nan wanda shi ne 4 ga Watan Nuwamba a fadar sa ta Aso Villa.
Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN tace Gwamnonin Yankin Kudu maso Yamman da su ka ziyarci Shugaban kasar sun hada da Mai Girma Gwamnan Jihar Ogun Sanata Ibikunle Amosun da kuma Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo.
Haka kuma Takwaran su watau Dr. Kayode Fayemi na Jihar Ekiti yana cikin wannan tafiya inda su ka shiga har ofishin Shugaban kasar su ka dauki lokaci su na tattaunawa. Har yanzu dai babu wanda ya san wainar da aka toya a fadar.
A halin yanzu dai Gwamna Ibikunle Amosun yana rikici da Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole game da wanda APC ta tsaida takarar Gwamna a Jihar. Shi ma dai Gwamna Rotimi Akeredolu yana rigima Oshiomhole.
Kwanan nan dai Shugaban kasa Buhari yayi ta ganawa da Jigon Jam’iyyar APC na Yankin Kudu maso Yamma watau Asiwaju Bola Ahmed Tinubu duk a kan abubuwan da su ke bijirowa a Jam’iyyar ta APC.
Sunday, 4 November 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
'yan sanda sun kama maza tare da takardun kuri'u 14 a Kano 'yan sanda sun kama maza tare da takardun k
Rahotanni na zaben shugaban kasar 2019 ya faraRahotanni na zaben shugaban kasar 2019 ya faraRah
Rahotanni na Live: 2019 Zaben Shugaban Kasa na Kasa daga Tsarin Gida A Nijeriya Na shekarar 2019Rahotanni na Live: 2019 Zaben Shugaban Kasa na Ka
Buhari, da matarshi Aisha Buhari sun fito domain kada kuri,a a Daura (hotuna)Buhari, da matarshi Aisha Buhari sun fito domain
Duba Kalmomi 7 masu karfi da Atiku ya furta a lokacin da akayi taron PDP NEC a yauDuba Kalmomi 7 masu karfi da Atiku ya furta a lok
SARAKI YAYI RANTSUWA A ALFA AS NEW KOGI-EAST SENATOR. SARAKI YAYI RANTSUWA A ALFA AS NEW KOGI-EAST SENA
0 Comments:
Post a Comment